A kwanan nan, hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da fasaha da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya, watau UNESCO ta kara rukunin wuraren sana’ar kayan tangaran na hannu na Jingdezhen da ke kasar Sin, a cikin jerin wuraren tarihi na duniya, inda hakan ya kawo jimillar muhimman wuraren tarihi na duniya da suka shiga kundin UNESCO a kasar Sin zuwa 61.
Sanya wurin wannan sana’a da Sinawa suka gada kaka da kakanni tsawon karnoni masu yawa a kundin UNESCO ya sake fayyace yadda riko da asali ya zama gadon Sinawa daga zurriyya zuwa zurriyya, saboda muhimmancin hakan ga wayewar kai da kuma kiyaye tarihi mai alfanu duk kuwa da sauye-sauyen zamani.
Wannan wuri wanda yake dauke da sirrin ci gaban kirkire-kirkire a fannin fasahar kasar Sin ta kera kayan tangaran da hannu, da fasahar tsara nau’o’in kayan tangaran, da kuma ita kanta masana’antar samar da su, ya yi matukar tasiri wajen bunkasar sana’ar kera kayan yumbu ko laka a duniya, da kuma bangaren cudanya da koyon juna tsakanin al’adu da wayewar kai mabambanta.
A duk nahiyoyin duniya, ire-iren wadannan kaya sun kasance tamkar wata alamar kasar Sin har ma wasu kan kira kayan da sunan kasar Sin baki daya.
Sanya rukunin wuraren sana’ar kayan tangaran na Jingdezhen a cikin kundin tarihin duniya zai kara inganta kiyaye karkon sana’ar da habaka cin gajiyarta ta fuskar yawon bude ido, saboda masu yawon shakatawa da dama da ba su san da wurin ba a baya, a halin yanzu za su sani, kuma wasu da dama, kamar ni da na taba ziyartar wasu wurare da ake sarrafa yunbu zuwa tukwane da sauran kayan laka a can gida Nijeriya, za mu so mu shaida irin yadda ake sana’ar kere-keren tangaran na kasar Sin mai dogon tarihi.
Wani na iya tambayar ta yaya Sinawa suka iya rike wannan sana’a tsawon kusan shekara dubu, bisa ga abin da na fahimta dai, gwamnatin kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen rayawa da kuma kiyaye sana’ar. Domin rigakafin shudewar sana’ar, gwamnati tallafa wa masu sana’ar, ta kafa cibiyoyin horaswa da gidajen tarihi domin matasa su ci gaba da koyon dabarun sana’ar ta gargajiya.
Kazalika, domin riko da asali, kasar Sin ta dukufa sosai wajen kula da dubban wuraren tarihi a fadin kasar wadanda suke tattarawa, da gyarawa, da kuma nuna kayan tarihi ga jama’ar kasa da masu yawon bude ido, abin da ke kara fahimtar da duniya tarihin kasar.
An sanya dokoki da hukumomi na musamman da ke hana rushe tsoffin wuraren tarihi ko safarar kayan tarihi ba bisa ka’ida ba.Ko da yake Sin tana samun saurin bunkasa ta fuskar tattalin arziki da fasahar zamani, amma ba ta wancakalar da tarihi da al’adunta na asali ba, domin ta yi amannar cewa, ci gaban zamani ba ya nufin mantawa ko binne tarihi da asali, bari ma dai, riko da asali mai kyau wani ginshiki ne na gina kasa mai karfin ci gaba. Sai dai fa, ba mai fahimtar hakan sai dan asali, domin riko da asali sai dan asali. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














