Ƙwararren likitan cutar daji (Oncologist), Dakta Bello Abubakar, ya musunta zargin ƙirƙirar takardar rahoton lafiya da ake zargin an yi amfani da ita wajen neman belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
A cikin bayanin, Dakta Abubakar ya amince cewa shi ne ya rubuta rahoton lafiyar, amma ya ce bai san mutumin da ake zargin ya yi amfani da rahoton wajen kai takardar shaida domin goyon bayan neman belin tsohon gwamnan ba.
Dakta Abubakar, wanda shi ne Babban Mai Ba da Shawara kan Cutar Daji da Maganin a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, ya rubuta bayanin ne ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC), a gaban lauyansa, Rabiu Suleiman na kungiyar lauyoyi Mahmud SAN and Co.
Ya ce, “Ban tuna da wani mai suna Mohammed Bala Aliyu ba, kuma ban taɓa ba shi umarni ko izini ya yi amfani da wata takardar shaida a madadina ba.”
A nata ɓangaren, ICPC ta gurfanar da Dakta Abubakar kan tuhume-tuhume huɗu, inda take zarginsa da bayar da rahoton lafiya na ƙarya da gangan domin yaudarar wani jami’in gwamnati da kuma taimakawa wajen neman belin Nasir El-Rufai a shari’ar mai lamba KDH/KAD/ICPC/02/2026, wadda ke gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna.














