Hukumar tattara kudaden shiga da raba kudaden shiga da kuma kasafin kudi (RMAFC) ta musanta rahotannin kafafen yada labarai na cewa, gwamnatin Nijeriya ta amince da karin albashin masu rike da mukaman siyasa da na shari’a da na gwamnati da kashi 114 cikin 100.
A wata tattaunawa ta musamman da LEADERSHIP, jami’in hulda da jama’a na RMAFC, Christian Nwachukwu, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu har yanzun bai rattaba hannu ba kan kudurin karin albashin ma’aikatan gwamnati.
Kwamishiniyar tarayya a hukumar, Rakiya Tanko-Ayuba ce ta sanar da amincewar karin albashin a lokacin da ta wakilci shugaban RMAFC, Mohammad Shehu, yayin da ta ke jawabi kan kwaskwarima da aka yi kan tsarin albashin ga gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, a ranar Talata a Birnin Kebbi.
Tanko-Ayuba ta ce, “an fara aiwatar da tsarin biyan albashin da aka yi wa kwaskwarima daga 1 ga watan Janairu, 2023”, wannan ikirarin, kakakin hukumar ya musanta shi da kakkausar murya.