Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma ta kori kocinta Ivan Juric sakamakon rashin nasara da ta yi a hannun Bologna a gida jiya Lahadi 3-2, wanda yanzu haka ta fara neman wanda zai maye gurbin shi.
An naɗa Juric ɗan ƙasar Croatia, mai shekaru 49 a watan Satumba a matsayin wanda zai maye gurbin Daniele de Rossi, wanda ya shafe watanni takwas ya na riƙon ƙwaryar jagorancin ƙungiyar bayan Jose Mourinho ya bar ta.
- An Dakatar Da Mourinho Wasanni 4 Kan Fada Da Alkalin Wasa
- Roma Ta Sallami Mourinho A Matsayin Kocinta
Tsohon kocin na Torino da Hellas Verona ya jagoranci wasanni 12 a Satde Olimpico, inda ya samu nasara a wasanni huɗu da rashin nasara a wasanni biyar.
Muna son gode wa Ivan Juric saboda kwazon da ya yi a makonnin da suka gabata, in ji masu ƙungiyar Roma The Friedkin Group, waɗanda ke tattaunawa yanzu haka don siyan ƙungiyar Everton ta ƙasar Ingila, sun cigaba da cewa an riga an fara neman sabon koci kuma ana sa ran sanarwa a cikin kwanaki masu zuwa.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon kocin Italiya da Manchester City Roberto Mancini ne ke jagorantar jerin ‘yan takarar bayan ya bar aikinsa na kocin ƙasar Saudiyya, Roma tana mataki na 12 a gasar Seria A kuma ta 20 a gasar Europa.