Shahararren dan wasan kwallon kafa da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr, Cristiano Ronaldo ya buga wasansa na 1,000 a tarihi a wasan da kungiyarsa ta doke abokiyar karawarta Al-Fayha a gasar zakarun yankin Asia da suka buga ranar Laraba.
Kwallon da Ronaldo ya jefa a ragar Al Fayha itace ta farko da ya jefa a wannan sabuwar shekarar ta 2024, kuma ta 746 jimillar kwallayen da ya jefa a raga a tarihin wasannin da ya buga a kungiyoyi 4 da ya zauna.
Kwallo daya tilo da Ronaldo ya jefa ta sa kungiyarsa ta Al Nassr tsallakawa zuwa matakin zagaye na 16 na gasar zakarun yankin Asia.