Shahararren dan wasan kwallon kafa mai taka leda a kungiyar Al Nassr da ke Saudiya Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasan da ya fi Kowa buga wasannin Kasa da Kasaa tarihin kwallon kafa.
Ronaldo ya kafa Wannan tarihin ne yayinda suka buga wasa da kasar Iceland a gasar cin kofin kasa da kasa na European Championship.
Ya samu kambun girmamawa na Guinness World Record kafin Fara wasan da ya jefa kwallo daya tilo da ta zama sanadiyar samun nasarar kasarsa a kan abokiyar karawarta.
A wasanni 200 da Ronaldo ya buga wa Portugal ya jefa kwallaye 123.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp