Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Kano, Haruna Isah Dederi ya bayyana kurakuran da ke kunshe cikin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige gwamna Abba Kabir Yusuf inda yace, hukuncin da kotun ta ayyana da baki ya sha bamban da tabbataccen Kwafin hukuncin da kotun ta mikawa gwamnatin Kano.
Ya bayyana haka ne da yammacin ranar Talata yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai kan hukuncin.
- Za Mu Kwato Wa Abba Hakkinsa A Kotun Koli – NNPP
- NNPP Ta Yi Maraba Da Kiran Atiku Na Dunkulewar Jam’iyyun Adawa Don Kauda APC
“An yanke hukunci game da dukkan kararraki hudu da muka daukaka, wanda mai girma Gwamna ya shigar, da karar da jam’iyyarmu ta NNPP ta shigar da karar da INEC ta shigar. Duk wadannan ukun an daukakasu ne saboda rashin amincewarsu da sakamakon hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a ranar 20 ga watan Satumba.
“karar ta hudu, itace wacce jam’iyyar APC ta yi. Duk waɗannan kararraki an sauraresu kuma an an yanke hukuncin kowacce.
“A ranar 17 ga watan Nuwamba, ranar Juma’a ne kotun daukaka kara ta karanta hukuncin. Wanda Yanzu haka kuma, aka bamu kwafin hukuncin daga kotun.
“Abin takaici dangane da karar da gwamna ya shigar, mun gano cewa, kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe.
“Ina ganin akwai tarko a nan. A yayin da muke zaman kotun an shaida mana cewa, an tabbatar da hukuncin da kotun farko ta yanke, amma a tabbataccen Kwafin takardun hukuncin game da daukaka karar da mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar kan jam’iyyar APC da wasu mutane biyu, ya nuna cewa, kotun ta jingine hukuncin kotun farko a gefe, hakan na kunshe ne a shafi na 67 na kwafin hukuncin.
“Har yanzu ba mu san hukuncin da aka yanke ba kenan dangane da korafe-korafenmu. Tuni dai lauyoyinmu suka fara daukar mataki dangane da hakan na shigar da kara a gaban kotun koli dangane da hukuncin kotun daukaka kara,” inji shi.
Ya bayyana cewa, da abin da ke kunshe a cikin Tabbataccen hukuncin da kotun daukaka kara ta ba su, Abba Kabir Yusuf shine halastaccen gwamnan jihar Kano kamar yadda kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe yanke a farkon watan Satumba.