Wani babban abin takaicin shi ne, sai aka wayigari majalisun Kasa wadanda na daga manyan aiyukan da suka rataya bisa wuyayensu, shi ne, yunkurin taka wa bangaren zartaswa birki game da duk wasu lamuran da za su cilla Tsarin Mulkin na Kasa ko al’umar Kasa cikin yanayi na benu, amma sai suka buge yin rufa-rufa daga mummunar yanayi na hadidiyar marga-margan basuka da fadar shugaban Kasa ke yi dare da rana!.
Irin waccan halaiya ta yin likimo bisa gaskiyar lamarin hakikanin basukan da shugaba Buhari ke ciwo wa Kasarmu ta gado, Nijeriya, ta yi sanadiyyar jefa wasuwasi cikin zukatan jama’a musamman masu bibiyar abubuwan da ka je su su zo. Ba za a yi dogon maimaici ba, a baya cikin wannan rubutu, akwai inda aka gabatar da wasu zarge zarge ga zauren ‘yan majalisun jiha da na taraiya, wajen nuna halaiyar ko in kula game da basukan da gwamnoni da shugaban Kasa ke ciwowa jama’ar Kasa, babu dare ballantana rana! Inda aka zarge su da;
- Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?
- INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi
i- Ko dai a na ba su makudan kudade ne na lasawa, shi ke sanya su saurin lamunta tare da kifuwa bisa ta’adar, su gani, su ki gani, kuma su ji, su ki ji, game da sha’anin irin wadancan malalar basukan da ake kan ciwo mana ba tare da kakkautawa ba!
ii- Cikin zargin nasu, a na yi musu duban marasa kishin kasa, sai na aljifansu!
iii- An kalle su da wadanda nauyaye nauyayen da ke bisa wuyayensu, ba su shirya sauke su ba!
ib- A na kallonsu da yunkurin fifita wata jam’iyar siyasa sama da kasarsu ta haihuwa!
b- Wasu ma na yi musu kallon gidahuman ‘yan dagaji ne kawai da ke dumama kujera!
bi- Wasu na kallonsu da wadanda makiya Kasa ke jan akalarsu daga can gefe, kasantuwar su ne ke daure musu gindin cin zabe, saboda haka, muradun irin wadancan shagalallun iyayen gidan nasu ne abin karewa, sabanin muradun Kasa!
bii- Mai yi wa, jahilcinsu ga hakikanin ilmin tattalin arzikin Kasa, shi ma ya fizge su zuwa ga afka Kasa cikin sukullufin tarin basukan da suka yi mata kabe kabe tamkar mai ciki na watanni tara (9)!
Duk da cewa mummunar son zuciya daga bangaren wadancan ‘yan majalisun, na da alaka ta kai tsaye ga nuna hali na shakulatin bangaro da suke yi ga batun yanayin bashin da yai wa Kasar kuri. Wata tambaya da shugaban Majalisar Dattijan wannan Kasa, Sen. Ahmad Lawan, yai wa shugaban kwamitin kudi na majalisa, Mr Solomon Adeola, a cikin Watan Satumbar Shekarar 2022, da kuma amsar tambayar, zai kara hakkakewa mai karatu yanayi na ‘yar burum burum da wasu ‘yan majalisun ke yi wa jama’ar Kasa. Babu shakka lokaci ya yi da al’umar mazabar Adeola da za su zargo shi da kunzumin kuru’unsu daga waccan majalisa su watsar, da ma sauran masu ra’ayi irin nasa!
A tambayar da Ahmad Lawan ya yi, ya nuna yanayi na rashin jin-dadi (duk da cewa a baya, shi ma ya ba da kai bori ya hau ga gwamnatin taraiya wajen hadidiyo basukan) da jama’ar Kasa ke da, na dalar gyadar basukan da ke neman haifar na yanayi na ‘ya kwance uwa kwance a Kasa. Sai Adeola ya amsa da cewa;
“The borrowing you’re saying is accumulated borrowings. It is not a borrowing of this administration alone, it is a borrowing that stems from the days of military to the days when the Democratic Dispensation started…”
Ga fassarar waccan amsa da Adeola ya bai wa takwarorinsa ‘yan majalisa kamar haka;
“Wannan bashi da ake ta babatu a kansa, basuka ne da suka samo asali tun daga lokacin mulkin soja a wannan Kasa, har kawo lokacin fara mulkin farar hula, sune fa jumla da suke ta kan ninkuwa, ba wai bashi ne da za a ce wannan gwamnati (ta Baba Buhari) ce kawai ta ciyo su”.
Adeola ya ci gaba da cewa, wai, ga dukkan naira sittin da bakwai (N 67) da suke biyan bashinta, to za a samu cewa sama da naira sittin (N 60 +…) daga adadin, na basukan da wasu gwamnatocin da suka gabata ne suke biya musu! Hoda! Allah Ya kiyashe mu afkawa cikin kalamai irin na kanzon kuregen Adeola!!!.
Mutumin da ke samo hujjojinsa daga teburin maishayi, ka iya afkawa cikin wasuwasi game da irin wadancan bakaken kalamai na Adeola, alhali shibcin gizonsa ne! Na’am, da wuya ne wai a ce ga wata gwamnati a Nijeriya, sawa’un ta Soja ce ko ta Farar Hula da za a ce ba ta ciwo bashi ba, a lokaci da take mirginawa. Sai dai, kididdiga ta ilmi da bin diddigi, sune kadai za su ware kwaya daga tsakuwa, wajen gano shin, wai wane shugaba ne daga cikin shugabannin Soja da na Farar Hula, wadanda suka fi taka mugunyar rawa ga zururun ramin basuka da Nijeriya ta afka ciki da keya?.
“Inside Nigeria’s Debts Crisis : How Foreign Loans Under Buhari Triples Past Gobernments Combined Figures”
Waccan matashiyar rubutu cikin Harshen Ingilishi, na kokarin gabatar da wata kididdiga ne da gidan Jaridar Premium Times ta fitar, a ranar 10 ga Watan Okotobar Shekarar 2021 (Premium Times, October 10, 2021) game da ninninkawar runbunan basukan shugaba Buhari, sama da na takwarorinsa sauran shugabannin wannan Kasa da suka gabace shi!. Cikin matashiyar, an yi isharar cewa, gwamnatin Baba Buhari ta ninka daukacin yawan adadin basukan kasashen ketare da gabadaya gwamnatocin da suka gabace ta suka ciwo har ninki uku!.
Mai karatu ya fahimta cewa, gwamnatocin da wancan gidan jarida na Firimiya ke nufin gwamnatin Buhari ta ninka yawan adadin basukan ketare har sau uku sune, gwamnatocin da wannan Kasa ta yi daga Shekarar 1999 zuwa 2015, wato gwamnatin Chief Olusegun Aremu Obasanjo (1999-2007), da gwamnatin Umaru Musa ‘yar Adua (2007-2009), sannan sai gwamnatin Dr Ebele Jonathan (2009-2015). Sai kuma shi Buharin, wanda ya damki madafun na iko, daga Shekarar 2015 har zuwa Shekarar 2023. Shi ne wani shugaba na Farar Hula da aka yi cikin tarihin Kasar, wanda sama da mutane dari (100) suka rasa rayukansu wajen kewayen murna, saboda lashe zabe da ya yi.
Shi ne shugaban da daukacin sako da lungu na birane da kauyukan Kasar, aka dinga aike masa da miliyoyin nairori tare da dari da kobo zuwa ga asusunsa na kamfen, kasantuwar a na ganin bai saci wasu makudan kudade daga lalitar Kasa da za su ishe shi yin yawon kafen a sako da lungu na Kasa bakidaya ba. Shi ne shugaban da manya manyan attajiran ‘yan siyasar Kasar suka narkarwa da mafi yawan madudan madarar kudade, da sunan gudunmuwa don ya samu ya lashe zaben kujerar shugaban Kasa.
Shi ne shugaban da duk wani talakan Kasar ya aminta da cewa zai amfani mamakon arzikin da Nijeriya ke da, wanda gabaninsa wasu gungun barayi ne ke ta wasoso dare da rana.
Shi ne wani dan takarar kujerar shugaban Kasa da aka taba yi a Kasar, wanda talaka ke daukar kadararsa mafi daraja, misali gida, ya sayar, kana ya aike masa da kudaden kacokan, don ya je ya yi hidimar kamfen da su.
Bisa yakinin talakan, bayan Buharin ya dare karagar mulki, zai sami sukunin sayan wani gidan ko ma wasu gidajen cikin sauki, tun da bawan Allah, Mr Clean ya sami nasarar shigewa cikin Billa da kunzumin halastattun kuru’u da jama’ar Nijeriya suka antaya masa. Shi ne…shi ne…shi ne…! Sai dai…sai dai…sai dai…!!! Bakina da goro tuli makil.