Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta soki matakin rufe makarantu a jihohin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi a lokacin Ramadan, tana mai cewa hakan ya tauye ‘yancin ɗalibai kuma yana barazana ga ilimi.
Matakin, wanda zai ɗauki makwanni biyar, yana shafar dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu, daga matakin firamare har zuwa jami’a.
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya ce an ɗauki matakin ba tare da tuntuɓar dukkan bangarori ba, kuma hakan na nuna wariya ga ɗaliban da ba Musulmai ba. Ya bayyana cewa ilimi haƙƙi ne na kowa, yana mai kira ga gwamnoni da su sake duba matakin don tabbatar da adalci da haɗin kai.
- Dan Majalisa Ya Kaddamar Da Ajujuwa 3 A Firamare A Adamawa
- Kashi 25% Na Makarantun Firamare A Kano Na Da Malami 1 Ga Duk Aji – LANE
CAN ta nuna damuwa kan yadda hutun zai dagula jadawalin karatu kuma ya ƙara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, wanda a yanzu ya kai kashi 44% a yankin. Ta ce a ƙasashen Saudiyya da UAE, makarantu na ci gaba da aiki a lokacin Ramadan tare da sauya jadawali, don haka babu dalilin rufe makarantu a Najeriya.
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnonin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi da su tattauna da shugabannin addini, iyaye da masu makarantu don samar da mafita mai ɗorewa. Ta kuma yi gargaɗi cewa, idan ba a gyara ba, za ta ɗauki matakin doka domin kare ‘yancin ɗalibai.
Archbishop Okoh ya buƙaci jama’a da su zauna lafiya tare da bin hanyoyin doka domin shawo kan lamarin. Ya ce CAN ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an samar da daidaito a tsarin ilimi, ba tare da nuna bambancin addini ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp