• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ruguntsumin Rantsar Da Sabuwar Gwamnati: Abubuwa 10 Da Suka Kamata A Sani

by Bello Hamza
2 years ago
sabuwar gwamnati

LABARAI MASU NASABA

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

Tun daga farkon makon nan ne aka shiga ruguntsumin rantsar da sabon zabbaben shugaban Nijeriya Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin shugaban tarayyar Nijeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi na shekarar 2023 in da ya lashe zaben da kuri’a 8,794,726 a takarar da ya yi a karkashin jam’iyyar APC. Bola Tinubu dai yana da shekara 70 a duniya a halin yanzu.

Ga wasu abubuwa 10 muhimmai da ya kamata al’umma su sani game da Shirin rantsar da zabbaben shugaban kasar da aka shirya yi a filin ‘Eagle Skuare’ da ke Abuja.

  1.  Ana sa ran bikin zai samu halartar shugabannin kasashe 54 daga kasashen Afrika da kuma shugabanin wasu kasashen su 65 da kasashen yankin nahiyar Turai, Amurka za su halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar.
  2. Za a gudanar da taron ne a filin taro na ’Eagle Skuare’ da ke Abuja.
  3. Wakilan kasashe abokan Nijeriya kamar Amurka, Birtaniya, Kanada, Faransa, Saudi Arebiya, UAE, Pakistan, Chana, Jamus, Finland, Jamaica, Japan, Israila da Turkiya za su halarci taron.
  4. An shirya karramawa ga zababben shugaban kasa Bola Tinubu wanda kuma shi zai zama shugaban rundunar sojojin Nijeriya da fareti na musamman na ranar Talata 23 ga watan Mayu.
  5. A ranar 24 ga watan Mayu aka gudanar da taron majalisar zartarwa na bankwana ga ministoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
  6. Za a gudanar da taro na musamman na motsa jiki wanda bangaren matasa na jam’iyyar APC suka shirya ranar 25 ga watan Mayu a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja za kuma a yi addu’a ta musamman a masallacin kasa a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu.
  7. Tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, zai gabatar da lacca a kan yadda za a yi amfani da dimokradiyya wajen bunkasa ci gaba al’ummar Afrika a ranar 27 ga watan Mayu.
  8. Faretin yara na ranar yara ta duniya zai gudana a ranar 27 ga watan Mayu, za kuma a yi addu’o’i na musamman a babbar cocin kasa ranar 28 ga watan Mayu.
  9. Bikin cin abinci da nuna al’adun gargajiya a babban dakin taro na fadar shugaban kasa ranar 28 ga watan Mayu.
  10. Za a yi taron cin abinci na musamman da shugabannin kasa da abokan zabbaben shugaban kasa kawai za su halarta a dakin taro na fadar shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu 2023.
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Next Post
…Waiwaye Game Da Yadda Aka Rantsar Da Wasu Shugabanni Na Baya

…Waiwaye Game Da Yadda Aka Rantsar Da Wasu Shugabanni Na Baya

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.