• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ruhin Yuan Longping Ya Ba Da Tabbaci Ga Samar Da Isashen Hatsi a Nahiyar Afirka

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Longping

Wannan ne takardar kudi mafi daraja a kasar Madagascar, inda aka zana shinkafar da aka tagwaita da Sin ta kirkiro.

Noman shinkafa shi ne aiki mafi muhimmanci a Madagascar, amma yawan shinkafar da kasar ke samarwa ba ya biyan bukatunta, duba da karancin fasahar zamani a wannan bangare, shi ya sa a baya ta kan shigar da dimbin shinkafa daga ketare a kowace shekara. Tabbatar da samun isashen hatsin, shi ne burin daukacin al’ummar kasar.

  • An Kaddamar Da Babban Filin Wasan Da Kasar Sin Ta Gina Wa Kasar Chadi Kyauta
  • An Kaddamar Da Babban Filin Wasan Da Kasar Sin Ta Gina Wa Kasar Chadi Kyauta

An yi wa mai nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin Yuan Longping lakabi da “Mahaifin shinkafar da aka tagwaita irinta a duniya”. Yuan Longping yana da muradu 2, daya shi ne nazari da samar da shinkafar da aka tagwaita irinta mafi armashi, dayan kuma shi ne samarwa duk fadin duniya irin wannan shinkafa. A shekarar 2006, karkashin jagorancinsa, tawagar Yuan Longping ta ziyarci Madagascar, ta kuma tagwaita irin shinkafar da ya dace da yanayin kasar, kuma sakamakon wannan nazarin da aka yi, yawan shinkafar da wannan nau’in iri ya samar ya ninka sau 3 bisa na nau’in iri da a kan samu a kasar a lokacin baya.

Yanzu, yawan shinkafar da Madagascar ke shukawa da samarwa, ya kasance kan gaba a nahiyar Afirka. Kuma ita ce kasa ta farko a nahiyar da ta kafa cikakken tsarin samar da shinkafar da aka tagwaita. Ba samar da isashen shinkafa ga manoma kadai aka yi ba, matakin ya taka rawar gani wajen tabbatar da burin samar da isashen hatsi a kasar.

A shekarar 2021, Yuan Longping ya riga mu gidan gaskiya. Tsohon babban sakataren ma’aikatar aikin gona ta kasar Madagascar Rakotoson Philibert ya ziyarci kabarin Yuan Longping dake lardin Hunan na Sin, tare da ajiye shinkafar da aka samar a kasarsa a gaban kabarin, don bayyana godiyar al’ummar Madagascar.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

A halin yanzu, a gonaki masu samar da shinkafar da aka tagwaita a Madagascar, ana farin cikin girbar shinkafa mai armashi. Masanan aikin gona na kasar Sin sun bi sahun Yuan Longping don tabbatar da burinsa na hadin gwiwa da manoman kasar wajen samar da isashen hatsi. (Mai zane da rubutu: MINA)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Fitaccen Fastan Kaduna Rabaran Azzaman Ya Mutu A Haɗarin Mota

Fitaccen Fastan Kaduna Rabaran Azzaman Ya Mutu A Haɗarin Mota

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.