Rukunin ba da tallafin jinya na Sin na 24 dake ba da agaji a jamhuriyar Nijar, da kwararru masu aikin hadin gwiwa na asibitin al’ummar jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai gashin kai ta kasar Sin da babban asibitin Nijar da Sin ta ba da taimakon gina shi, sun gudanar da aikin jinya kyauta da wayar da kan jama’a a ranar 18 ga Nuwamban nan.
Farfesa Mamane Daou, shugaban babban asibitin Nijar, ya ce irin wannan hadin gwiwa da Sin ba kawai yana kara karfafa amincewa tsakaninsu ba, har ma yana kafa tushe mai karfi ga hadin gwiwarsu na nan gaba, wanda zai karfafa ingancin tsarin kula da lafiya mai dorewa a Nijar.
Shugaban rukunin ba da tallafin jinya a Nijar na Sin na 24, Zheng Zhida, ya bayyana cewa wannan aikin da aka gudanar ya bayyana ruhin masu aikin jinya na Sinawa wato “rashin tsoron aiki mai wahala, sadaukarwa, ceton rayuka, da babbar kauna mara iyaka”, kuma shi ne kyakkyawar alamar abota tsakanin Sin da Nijar a fannin kiwon lafiya. (Amina Xu)














