Rukunin sojoji injiniyoyi na tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin karo na 25 dake kasar Congo Kinshasa, ya kammala aikin gyara titi, wanda ya dauki tsawon watanni 8 yana yi cikin nasara.
Yanayin damina ya lalata titin mai tsawon kilomita 96 dake tsakanin yankin Uvira da yankin Baraka na kudu maso gabashin kasar Congo Kinshasa, inda yake kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa da ta jama’a a yankin.
Bisa rokon sashen ba da umurni na tawagar musamman ta MDD dake kasar Congo Kinshasa wato MONUSCO, rukunin sojoji injiniyoyi na tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Sin, ya fara aikin gyara titin a cikin watan Febrairun bana.
Bayan aikin da aka yi na tsawon watanni kimanin 8, sojojin kasar Sin sun tunkari kalubalen yanayi maras kyau, da cututtukan dake bazuwa a kasar, da kuma halin tsaron, inda suka cimma nasarar gyara titin dake tsakanin Uvira da Baraka, da kuma farfado da zirga-zirgar ababen hawa a yankin. (Zainab)