Rundunar Ƴansanda ta kasa ta ɗauki matakin gaggawa bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna jami’anta suna karɓar cin hanci daga direbobi.
A cikin bidiyon da ya bazu sosai a ranar Litinin, an ga wani Dansanda yana neman direbobi su ba shi ko dai Naira 5,000 ko kuma lita 5 na man fetur idan ba su da shaidar rajista da Electronic Central Motor Registry (e-CMR).
Da yake mayar da martani kan lamarin, mai magana da yawun rundunar Yansanda, Olumuyiwa Adejobi, ya yi tir da lamarin cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X (Twitter).
Adejobi ya ce, “Wannan abin kunya ne kuma ba za a amince da shi ba. An gano waɗanda suka aikata ]wannan mummunan aiki kuma an gayyace su zuwa shalkwatar Ƴansanda domin ɗaukar matakin ladabtarwa. Ba za mu lamunci duk wani nau’i na rashin da’a ko rashin ƙwarewa ba.”
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa za a ci gaba da sanar da su mataki da bincike da kuma hukuncin da za a ɗauka a kan jami’an da suka aikata laifin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp