Rundunar ƴansanda ta Jihar Kano ta kama wasu mutane tara da ake zargi ƴan ƙungiyar barayi ne da ke tare hanya don aikata ta’addanci a Kano, da Kaduna har ma da Abuja. Kwamishinan Ƴansanda na jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a shalƙwatar rundunar da ke Bompai a Kano.
Bakori ya ce an kama mutanen ne bayan wani harin fashi da makami da ya faru a Unguwar Wambai, Dorayi Babba, a ranar 8 ga Oktoba, 2025, inda ƴan fashin suka kutsa cikin gidan da misalin ƙarfe 2 na dare, suka yi wa matar gidan rauni, sannan sukarta, suka kuma tafi da mota kirar Toyota Yaris, da kuɗi har miliyan₦3.7, da wayoyi da wasu kayan alfarma.
- Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
- Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
Bayan samun rahoton gaggawa daga ofishin Dorayi, nan take rundunar ƙarƙashin jami’an SIS suka kama mutum ɗaya wanda bayan bincike ya kai ga cafke sauran abokan aikinsa guda takwas a Kano da Kaduna. Kwamishinan ya lissafo sunayensu da suka haɗa da: Abubakar Aminu (22), da Aliyu Aliyu (23), da Abubakar Usman (22), da Sulaiman Sani (20), da Yusuf Yusuf (17), da Abdulrahman Aliyu (23), da Salisu Hussaini (17), da Sulaiman Abdullahi (20), da Abdulmutallib Sa’ad (24).
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da bindiga mai sinƙi biyu da harsasai 18, da bindigogi guda biyu, da wuka, da Adda, da ƙarfen yankan ƙofa, da fitilu uku, da kuma mota ƙirar Toyota Corolla da suke amfani da ita wajen aikata laifuka. Bakori ya ce sun amsa laifin aikata fashi a jihohin Kano, da Kaduna da kuma Abuja, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ya ƙara bayyana cewa shirin “Operation Kukan Kura” na rundunar ya taimaka matuƙa wajen rage laifuka a Kano, musamman fashi da satar waya. Ya kuma yaba wa jami’ansa bisa jajircewa da ma jama’ar gari bisa bayar da bayanai masu amfani wajen kamo masu laifi.