Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan ya tabbatar da mutuwar Ƴansanda huɗu da Sojoji uku jiya Alhamis da bayan da ƴan bindiga suka yi masu kwantan ɓauna lokacin da Ƴansandan ke ƙoƙarin kare wasu ƴan ƙasashen waje ma’aikatan hanyar titin Gusau Zuwa Funtuwa da suke ƙoƙarin garkuwa da su.
Kwamishina Dalija ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a gidan Gwamnati da ke Gusau .
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Rabon Naira Biliyan 11 Na Bunkasa Ilimin Mata A Jihar
- Ƴan Bindiga Sun Tare Hanyar Zamfara, Sun Sace Matafiya 150
Dalijan ya tabbatar da cewa, wannan kisan Jami’an tsaro ba zai karya masu guiwa ba akan yaƙi da ƴan bindigar da suka addabi al’umar Jihar Zamfara ba.
Shi ma a nasa jawabin Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya miƙa ta’aziyarsa ga rundunar Ƴansanda da ta Soja a kan rasa jami’ansu sakamakon artabu da ‘yan dindigar.
Gwamna Dauda ya tabbatar da cewa, gwamnati zata yi iyaka ƙoƙarin ta wajan ganin an tallafawa iyalan jami’an tsaron da suka rasu wajan kare al’umma.