Rundunar jami’an tsaro ta farin kaya (NSCDC) a jihar Kano ta cafke Basiru Ahmed dan shekaru 42 da haihuwa bisa zargin laifin hada-hadar miyagun kwayoyi da ake kyautata zaton tabar wiwi ce har kulli 106 a jihar.
Kakakin Rundunar, SC Ibrahim Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Salanta da ke karamar Hukumar Gwale ta Jihar bayan samun bayanan sirri.
- Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
- Matar Marigayi MKO Abiola, Ta Rasu Tana Da Shekaru 82
Abdullahi ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake sayarwa da rarraba haramtattun abubuwa a cikin al’umma.
Ya kuma bayyana cewa, tuni aka mika wanda ake zargin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp