Rundunar Sojojin Nijeriya ta tura dakarun runduna ta 12 zuwa garin Olle-Bunu da ke ƙaramar hukumar Kabba/Bunu a Jihar Kogi domin yaƙi da matsalar ‘yan bindiga da ke addabar yankin.
Tura dakarun ya biyo bayan bayanan sirri da suka nuna shirin wasu ‘yan bindiga da suka yi ƙaƙa-gida a yankin.
- Mutuwar Malamin Jami’a A Otel: Jami’ar Kogi Za Ta Gudanar Da Bincike
- Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Gidan Sanata Natasha A Kogi
Rundunar ta ɗauki wannan matakin ne lokacin da mai bai wa Gwamna Usman Ododo shawara kan harkar tsaro, Kwamanda Duro Jerry Omodara (rtd), ya kai ziyarar duba yanayin tsaro a yankin.
Omodara ya aika da saƙo mai ƙarfi ga masu aikata laifi, yana mai jaddada cewa, “Jihar Kogi ba za ta saurara wa ‘yan ta’adda ba.”
Wannan matakin yana cikin sabon matakan da Gwamna Ododo ya ɗauka na tsaurara matakan tsaro a faɗin jihar.
Tun da farko, an rufe wuraren da ake zargi a matsayin maboyar ‘yan bindiga, kamar a Odo-Ape ta hanyar haɗin guiwa da jami’an tsaro mafarauta da kungiyar sa-kai. Garin Olle-Bunu ya zama wata mafaka ga ‘yan bindigar da aka koro daga wasu yankuna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp