Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama wani Kwale-kwale dauke da wasu kulli da ake zargin muggan kwayoyi ne a Ibeshe, Iworo da Badagry a jihar Legas.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Sub Lieutenant Happiness Collins ya fitar, ya ce, a kiyastacce, kwayoyin sun kai Naira miliyan 200, nauyinsu ya kai kilo 2,640.
- Tirka-tirkan Takardun Tinubu: Ku Zo Mu Hada Hannu Don Fafutukar Wanzar Da Gaskiya – Atiku Ya Roki Obi, Kwankwaso
- Minista: Magajin El-Rufai Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Majalisa
“Duk da cewa, wadanda suka yi kokarin shigowa da kayan, sun tsere bayan hango jami’an sojin, amma an kwace kayayyakin tare da mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin daukar matakin da ya dace.” inji sanarwar.
Collins ya kuma bayyana cewa, Kwamandan rundunar sojin ruwan da ke sintiri a yankin (NNS BEECROFT), Commodore Kolawole Oguntuga, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton sirri ga jami’an tsaron domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda.