Rundunar Sojin Nijeriya ta yi wani gagarumin tarihi inda ta ƙarawa Laftanar na biyu Oluchukwu Owowoh mukamin Laftanar na ɗaya, biyo bayan umarnin da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayar.
Sanarwar da aka fitar ta hannun Kwalejin tsaro ta Nijeriya (NDA) ta bayyana irin nasarorin da Laftanar Owowoh ta samu a yayin wani bikin ƙarin girma da aka gudanar a NDA. Manjo Janar JO Ochai, Kwamandan NDA, ya yaba da kwazon da ta yi ya kuma nuna farin cikinta a matsayin jami’ar Nijeriya mace ta farko da ta samu horo a babbar makarantar soji ta Royal Military Academy Sandhurst da ke ƙasar Ingila.
- An Fara Atisayen Soja Na Hadin Gwiwa A Kewayen Tsibirin Taiwan
- Kaico: Wani Sojan Ya Bindige Kansa Har Lahira A Ƙofar Bariki
Bikin ƙarin girman ya samu halartar manyan jami’an Soji, da malamai da ma’aikatan ilimi, ƴan uwa, da manyan baƙi, wanda hakan ya nuna muhimmancin nasarar da Laftanar Owowoh ta samu. Ta fara ne da kammala karatun ta na tarihi daga Royal Military Academy Sandhurst a cikin watan Afrilu, inda ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko a Nijeriya da ta kammala wannan gagarumin horo.
Taron dai ya kasance a wani muhimmin lokaci a tarihin Sojan Nijeriya, wanda ke nuni da irin himmar da Sojoji ke da shi na karramawa masu nuna bajinta don haɓaka hazaƙa a tsakanin jami’anta, musamman mata da ke cikin Sojoji.