Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta karyata rahoton harin da aka kai kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a yayin gangamin yakin neman zabe a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Laraba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Abdu Umar ne ya bayyana hakan ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Sani Shatambaya, wanda ya bayyana labarin a matsayin labaran karya da masu neman yada fitina suka yada musamman a shafukan sada zumunta.
Shatambaya ya ce, “Kwamishanan ‘yan sanda mai kula da rundunar ‘yan sandan jihar Borno, CP Abdu Umar, yana so ya jaddada cewa ba a kai wa ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP hari ba a yayin gangamin yakin neman zaben da aka gudanar a jihar a ranar 9 ga Nuwamba, 2022.
“An gudanar da yakin neman zaben cikin nasara, sabida an dauki tsauraran matakan tsaro a duk lokacin da ake gudanar da ayyukan, an baza jami’an tsaro ta ko’ina a yayin gangamin, sai dai, an kama wani Danladi Musa Abbas mai shekaru 32 a lokacin da ake gudanar da gangamin da laifin haifar da wani dan karamin rikici a hanyar airport road, sai wasu masu yada jita-jita suka kara ta’azzara rahoton hakan kamar yadda ake ta yadawa.
“Sabida haka, kwamishinan ‘yan sanda, CP Abdu Umar, ya yi kira ga sauran jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a jihar da su daina yada labaran karya da za su iya kawo cikas ga zaman lafiyan da ake samu a jihar, musamman ganin yadda babban zaben 2023 ke gabatowa.”