Rundunar ‘yansandan Nijeriya, ta gayyaci DSP Aliyu Adejembi da abokan aikinsa da aka gani a wani faifan bidiyo, suna karbar kudade daga hannun ‘yan Chana zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja, domin amsa tambayoyi.
Bidiyon da ya fito a shafin sada zumunta a ranar Talata, ya nuna wasu ‘yan kasar Chana da ke raba kimanin Naira 5,000 ga kowane dansandan Nijeriya a cikin jerin gwano.
- Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
- Alkaluman Tattalin Arzikin Sin Sun Shaida Dorewar Ingancin Tattalin Arzikinta
Wannan al’amari da ya faru, ya yi matukar tayar da kura tare da cece-kuce a shafin yanar gino, inda mutane da dama suka nuna rashin jin dadinsu tare da yin kira ga rundunar ‘yansanda, domin daukar kwakkwaran mataki.
Binciken da LEADERSHIP ta tattaro ya nuna cewa, ‘yansandan sun yi wa ‘yan kasar Chanan rakiya ne a wani wuri da ke cikin Jihar Kaduna.
“Daga labarin da na samu a wurin abokan aikina daga tsohon ofishin da na bari, an tura ‘yansandan ne domin bai wa Ma’aikatan Sinawan tsaro. Bayan sun kammala aikin, sai Sinawan suka yanke shawarar kyautata musu ta hanyar raba musu kudade”.
“Maimakon ya bai wa babban jami’in nasu kudin ya raba wa mutanensa, sai ya zabi rarraba musu shi da kansa”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wannan jarida.
Sai dai, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gayyaci ‘yansandan ne zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin ladabtar da su.
An gayyaci jami’in da sauran yaransa zuwa hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja, domin daukar matakan ladabtarwa, in ji majiyar.
Kamar yadda siginal mai dauke da kwanan wata na ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, wadda LEADERSHIP ta samu, ya nuna cewa; ‘yansandan da shugaban tawagarsu, DSP Aliyu Adejembi, za su bayyana a hedikwatar ‘yansan da ke Abuja, domin amsa tambayoyi kan rashin da’a da kuma gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp