Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta ce, a yanzu haka ta dukufa amfani da wasu sabbin dabarbarun aiki ta hanyar amfani da fasahar sadarwar zamani wajen taso keyar masu garkuwa da mutane da suka addabi jama’a.
Rundunar ta ce, tunin ta ma fara amfani da tsarin kuma an samu nasara har ma an cafko wasu mutum uku da suka kitsa da shirya aikata garkuwa da mutane wato Haro Adamu mai shekara 35, Aliyu Saidu mai shekara 40 da kuma Musa Umaru dan shekara 35 dukkaninsu mazauna birnin Kudu ta jihar Jigawa.
- An Gabatar Da Rahoton Binciken Kamfanonin Sin Game Da Halinsu Na Zuba Jari a Ketare a 2023
- Zulum Ya Ba Da Tallafin Fetur Ga Manoma Don Habbaka Noman Rani
Wadanda ake zargi masu garkuwan ne sun shiga hannun ‘yansanda ne a Birnin Kudu ta Jigawa da Kaltunga ta jihar Filato ta hanyar amfani da sabbin na’urorin fasahar zamani.
A wata sanarwar da kakakin rundunar SP Ahmad Muhammad Wakil ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, wani mutum ne mai suna Yahaya Adamu daga kauyen Badakoshi a jihar Bauchi ya kai korafin cewa wani mutum ya kirasa inda ya masa barazarar cewa muddin in bai hada masa naira miliyan biyar ba, to zai sanya shi da yaransa su zo su yi garkuwa da shi ko iyalansa.
Bayan hakan, kwanaki kalilan sai shi mai kiran wayar ya tura ma Yahaya asusun ajiyar banki ta hanyar amfani da asusun kasuwanci na POS da cewa ya tura kudin a ciki ko a sace shi da iyalansa.
Wakili ya ce, masu garkuwan sun ce sun sanshi sun san kadarorinsa sun san iyalansa don haka kar ma ya yi yunkurin ki bin umarninsu, muddin yayi hakan kuma zai gani.
A cewar sanarwar nan take bayan amsar rahoton jami’an sashin kula da manyan laifuka suka bazama amfani da hanyoyin zamani domin dakile aniyar bata garin.
“Mun yi amfani da fasahar zamani wadanda ba za mu bayyanasu ba saboda kar masu aikata laifin su gano sabbin hanyoyin da muke yi, amma ina tabbatar muku cewa sabbin dabaru ne da ke taimaka mana sosai wajen dakile masu aikata laifuka,” ya shaida.
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya da zarar aka kammala gudanar da bincike.