Rundunar ‘Yansandan Jihar Kebbi ta karawa jami’anta 52 mukami zuwa matsayin mataimakan Sufiritanda na yansanda (ASP II) a rundunar yansandan jihar Kebbi.
Karin girman wanda hukumar kula da aikin ‘yansanda (PSC) ta amince da shi bisa shawarar babban sufeton ‘yansanda IGP Kayode Adeolu Egbetokun, kwamishinan ‘yansanda CP Bello M. Sani ne ya yi masa ado da sabon Karin girman a ranar Alhamis 15 ga watan Agusta 2024.
- Gwamnati Za Ta Samar Da Tsaro A Filayen Hakar Ma’adanai —Alake
- Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta
CP Bello M. Sani ya taya jami’an da suka samu karin girma murna, inda ya bayyana karin girma da aka yi musu a matsayin wani abu mai matukar farin ciki tare da alfahari da kuma “babban canji a cikin aikinsu na dansanda.
“Ya umarce su da su kasance masu ladabtarwa, ƙwararru, da farar hula ga jama’a, tare da jaddada buƙatar daidaita matakin da’a da adalci.
jami’an dai da suka samu karin girma sun godewa CP bisa irin wannan karamci da kuma soyayar da kauna da ya nuna na a matsayin shi ma uba, inda suka yi alkawarin kara kaimi wajen sauke nauyin da aka dora musu.
Bikin Karin girman dai ya gudana ne a hedikwatar yansanda jihar da ke Gwadangaji, Birnin Kebbi, kuma ya samu halartar jami’an gudanarwa da ke Mataimaka ga CP. Muhammad Bell Sani
Ana sa ran wannan ci gaban zai kara wa jami’an kwarin gwiwa da kuma kara kwazo ga jami’an rundunar ‘yansandan ta jihar Kebbi wajen tabbatar da doka da oda a jihar.