Kusan shekaru shida kenan ana ci gaba da bibiyar karar, rundunar ‘yansandan jihar Kano ta cafke na gaba-gaba kan zargin aikata laifin kisan kai a shekarar 2018.
Cafke Magaji Yallo, mai shekaru 38, babbar nasara ce kan binciken kisan da aka yi wa Gausu Umar Sadau, mai shekaru 35, wanda aka yi wa kisan gilla a karamar hukumar Minjibir ta jihar.
- Ba Wanda Zai Yi Zanga-zanga A Bauchi – Muhammad Ibrahim
- Masana Sun Nemi Gwamnati Ta Rage Wa Kananan Masana’antu Haraji
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli, 2024, inda ya ce, lamarin wanda ya faru a ranar 10 ga watan Agustan 2018, wani mazaunin garin Kunya ne ya sanar da rahoton ga ‘yansanda.
Rahoton ya ce, Yallo da wasu ne suka kai wa Sadau hari da muggan makamai, inda suka yi masa munanan raunuka, ciki har da yanke masa jijiyar kafa.
Nan take aka kai Sadau asibiti amma jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsa.
Binciken farko ya kai ga kama wasu mutane biyu, Rabiu Sarki Lota da Nasiru Adamu Namade, wadanda ake tuhuma da laifin hada baki da kuma kisan kai.
Duk da wadannan kamen, babban wanda ake zargin, Yallo, ya ci gaba da tsarewa hukuma kusan shekaru shida sai yanzun ya shigo hannu.