Jama’a barkanku da wannan rana ta Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a, shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba, musamman na kuruciya. Yau ma shafin na tafe da sakonnin da kuka aiko mana kamar haka:
Sako daga Zainab Bello Yakasai Jihar Kano:
Ina gaida Mamana Haj. Habiba, da kanwata Maryam Bello, Jamila Bello, Shafa’atu Bello, Shehu Bello, Auwalu Bello, Amina Bello, Salamatu Bello, sai babbar yayata Aisha Bello, da fatan sun yi juma’a lafiya. Ba zan manta da ‘Ya’yana ba kamar su Khadija Muhammad Inuwa, sai wata Khadija Muhammad Inuwa, da Ibrahim Muhammad Inuwa, da Abdulbaki Muhammad Inuwa, sai Abbas M.Inuwa, sai kuma Maryam M.Inuwa da fatan su ma sun yi juma’a lafiya.
Sako daga Zainab Haruna Umar Unguwar Kawo Jihar Kano:
Sakon goron juma’a zuwa ga sahibina, masoyina, muradin ruhina, uban ‘ya’yana, farin cikina, wanda duk duniya ba ni da kamar sa bayan iyayena, me suna mai tsada wato Abubakar Muhammad Baba Yaro, fatan alkhairi tare da sakon goron juma’a zuwa gare shi abin alfaharina, da fatan yayi juma’a lafiya, Allah ya karawa rayuwa albarka.
Sako daga Rahma Ibrahim Jihar Kaduna:
Ina gaida kawata Maryamu da kanwata Saudat, da Kareema da Zulfa, ina gaida Leemat ina gaida Sadeek ina gaida sauran kawayena da abokaina baki daya, ina fatan sun yi juma’a lafiya.
Sako daga Kabeer Iliyasu Jihar Katsina:
Ina gaida Masoyiyata Zeenat Idris, ina gaida mahaifana da kannena, da Malamanmu na boko da islamiyya, ina gaida abokina Hashim, da fatan za su yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Aishat Isma’il Jihar Kano:
Asssalamu alaikum jaridar Leadership ina son a mikan sakon goron juma’a zuwa ga kawayena ‘yan makarantan mu da gaba daya ‘yan ajinmu kar su Hauwa Jibrin, Baby Beauty, Zeey Ahmad, Fauziyya Shazali, Hibbah Chas, da sauransu duk ina gaishe su, kuma da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Maryam Ibrahim (Hamshakiya):
Ina gaida Hajiya Kulu da Haj. Ababa da Auntyna Zulaihat, da wata Auntyn tawa Haj. Binta, ina gaida kannena baki dayansu kamar; Aliyu, Tahir, Hajjiyannan, Mummy, Ikleema, da sauransu ina gaida gaba daya al’ummar musulmi, da fatan kowa zai yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Abdulfata Ibrahim Zaria:
Ina yi wa dukkanin ‘yan uwa musulmai fatan Alkairi da fatan za a yi Sallar juma’a lafiya, Na gode.