Jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya yi gargadin cewa; rugujewar jam’iyyar na nuna babbar barazana ga demokuradiyyar Nijeriya.
Lamido ya gargadin cewa, yukurin raunana babbar jam’iyyar ta adawa da sauran makamantanta a Nijriya, ya yi kama da kokarin durkusar da tsarin demokuradiyyar kasar.
- Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
- Kasar Sin Ta Yi Kiran Kawar Da Makaman Nukiliya Bisa Tsarin Tsaro Na Bai Daya
Tsohon Ministan Harkokin Waje a lokacin Gwamnatin Olusegun Obasanjo, ya koka da cewa; ci gaba da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya APC mai mulki, zai iya cutar da makomar demokuradiyyar Nijeriya.
“Murkushe ‘yan adawa tare da musguna musu, musamman jam’iyyar PDP, wata alama ce karara da ke nuna cewa; zangon karshen mulki na karatowa; domin kuwa tarihi ya sha nuna hakan”, in ji Lamido a tattaunawarsa da BBC Hausa.
“Ya kamata Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kasance mai adalci, domin shi ne shugaban dukkanin ‘yan Nijeriya. Dole ne ya bar ‘yan adawa su yi takara a siyasance da jam’iyyar APC, idan kuma bai yi taka-tsan-tsan ba, abin zai iya komawa kansa”, in ji shi.
A ranar Litinin ne, Gwamnan Jihar Delta Sheriff Oborebwori da da wanda ya gaji kujerar daga wajensa, Dakta Ifeanyi Okowa da daukacin tsarin ‘yan siyasar da ke jam’iyyar PDP a jihar, suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Haka zalika, a makwannin da suka gabata ne, ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyun adawa irin su LP da NNPP, su ma suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Sannan kuma, ana samun rade-radin cewa, gwamnonin jihohi da dama na shirin yin koyi da shi,
A halin da ake ciki yanzu, bayan wani dogon zama da kwamitin gudanarwar PDP na kasa ya yi, jam’iyyar PDP ta kudiri aniyar kwato ragamar shugabancinta daga hannun wadanda suka sauya sheka.
Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Ambassador Illiya Umar Damagum, da yake jawabi bayan kammala taron nasu, ya ce; jam’iyyar ta umarci mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na kasa, ya fara shiri don tunkarar wannan kara.
Damagum ya bayyana cewa, jam’iyyar ta amince da shawarwarin da gwamnonin PDP suka bayar a taron da suka gudanar a Ibadan kwanan nan, wanda ya hada da nadin sabon Sakatare na kasa da kuma tsara babban taron jam’iyyar na kasa nan gaba.
Da yake tsokaci kan sauya sheka na Delta, Damagum ya ce; ya ji dadin yadda gwamnan da tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ba su soki jam’iyyar ba, ya kara da cewa; babu wani abu da jam’iyyar ta yi musu da ya sa suka bar ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp