Wani yaro dan shekara 15 da aka bayyana sunansa da Sallah ya gamu da ajalinsa yayin da wani gini da ya rufta a hanyar Shiroro, Minna, babban birnin Jihar Neja.
Shaidu sun shaida wa cewa matakalar ginin ce ta fado a kan yaron.
Wani dalibin makarantar Islamiyya da ke yankin Sallah, an ce yana hutawa ne tare da abokansa biyu a lokacin da lamarin ya faru, kuma ya mutu nan take yayin da daya daga cikin abokansa ya samu raunuka.
Daya daga cikin mazauna yankin, Jabir Ayuba, ya shaida wa wakilinmu cewa ginin da aka shafe shekara daya ana gina shi ba shi da takamammen bayanai.
“Mun damu tun da aka fara ginin wannan bene. Yaron da ya mutu yana tare da mu a safiyar yau; har ma ya gaya mana yana son siyan katin waya don kiran mahaifiyarsa a kauye.
Shi makwabcinmu ne. Yana zaune a nan shi da abokansa guda biyu, sai matakin ginin ya rufta a kansa, ya mutu nan take.”
Tuni dai Hukumar Raya Birane ta Jihar Neja ta sanya alamar rushe ginin kafin ya karasa rushewa.
Kokarin jin martanin mai ginin ya ci tura, bayan da aka ce yana Abuja.