• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rushewar Masa’antu Ya Jefa Al’umma Da Dama Cikin Ƙangin Talauci A Arewacin Nijeriya

by Rabi'u Ali Indabawa
48 minutes ago
in Manyan Labarai
0
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A cikin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta wajen ci gaban masana’antu ciki har da giɓin fasaha da kayan more rayuwa, da kuma ƙarancin jari, masana’antu a Arewacin Nijeriya sun ƙara fuskantar matsalolin manufofi tare da zama cikin rashin tabbas, rashin kulawa mai ɗorewa, matsalar wutar lantarki, sufuri, da sauransu. Wannan ya jawo rushewar masana’antu da dama, sakamakon dogaro ga man fetur da kuma kuɗaɗen da ake samu daga gwamnatin tarayya.

Wakilanmu sun gudanar da wani bincike kan halin da masana’antu ke ciki a jihohin Arewa. Sakamakon binciken da zo da abin mamaki.

KWARA

Kamfanonin masu zaman kansu da suka durƙushe a Jihar Kwara sun haɗa da: Global Soap and Detergent Industry, Ilorin; Nefraday Farms Nigeria Limited; Okin Biscuits Nigeria Limited; Ijagbo Noble Breweries Nigeria Limited, Ijagbo; da kuma PANAT Feeds Nigeria Limited.

Kamfanonin gwamnati na jiha da suka lalace kuma sun haɗa da: Tate and Lyle Nigeria Limited, Ilorin; Kwara Teɗtile Limited; Kwara Commercial Metal and Chemical Industry; Erin-Ile Paper Conɓerter, Erin-Ile; da Matches Manufacturing Company, Ilorin.

Labarai Masu Nasaba

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

Haka kuma, kamfanonin gwamnatin tarayya da suka durƙushe a jihar sun haɗa da: Nigeria Paper Mill, Jebba; Nigeria Sugar Company, Bacita; da Nigeria Yeast and Alcohol Manufacturing Company, Bacita.

  • Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi
  • Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi

Jaridar LEADERSHIP Sunday ta gano cewa wasu kamfanonin gwamnati na jihohi sun riga sun durƙushe tun kafin zuwan tsarin mulkin dimokuraɗiyya na yanzu a Nijeriya a shekarar 1999.

Haka kuma, an gano cewa wasu kamfanonin masu zaman kansu sun durƙushe ne sakamakon manufofin gwamnati marasa kyau, mawuyacin yanayin tattalin arziƙi, wutar lantarki mai yawan ɗauke wuta, shigowar kayayyaki marasa inganci, hauhawar farashin kayayyaki, tashin farashin kuɗin ƙasashen waje, da kuma rashin ingantaccen tsarin shugabanci.

An ruwaito cewa an kafa wasu sabbin kamfanoni daga gwamnatin jiha da kuma ƴan kasuwa masu zaman kansu tun bayan nan, kuma suna ci gaba da bunƙasa.

Sabbin kamfanonin da gwamnatin Jihar Kwara ta kafa sun haɗa da: Kamfanin ‘Ilorin Innoɓation Hub, Garment Factory, da Sugar Film Studio Factory.

Daga cikin kamfanonin masu zaman kansu da ke bunƙasa a jihar akwai: KAM Holdings Ltd (masana’antar sarrafa ƙarfe), Tuyil Pharmaceutical, Ilorin, Dangote Flour Mills, Forgo Battery Company, Ilorin, Peace Standard Pharmaceutical Industry, Bioraj Pharmacy, da Rajrab Pharmacy.

Kwamishiniyar harkokin Kasuwanci, Ƙirƙire-ƙirƙire da Fasaha ta jihar, Hajiya Damilola Adelodun-Yusuf, ta bayyana cewa kamfanonin masu zaman kansu na bunƙasa ne sakamakon aiwatar da manufar sauƙaƙe harkokin kasuwanci ta gwamnatin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaƙ.

Ta jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su ƙara haɓaka masana’antu a jihar.

Tsohuwar shugabar ƙungiyar KWACCIMA, Oluronke Adeyemi (SAN), ta ce za su ci gaba da tattaunawa da hukumomi masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa juyin juya halin masana’antu da kuma inganta ci gaban tattalin arziƙin jihar.

Ta ce: “Shekaru da dama kenan muna fuskantar ƙalubale da yawa, kuma mun san cewa gwamnati ba za ta iya magance komai cikin shekara ɗaya ko biyu ba. Amma muna tabbatar da cewa gwamnati tana ci gaba da aiki kan waɗannan matsaloli, domin a hankali wasu daga cikin matsalolin da ke damun masana’antun za su zama tarihi.”

 

GOMBE: Masana’antun da suka durƙushe har yanz

u suna nan a lalace

A Jihar Gombe, manyan masana’antu da dama suna rufe ko kuma ba sa aiki, ciki har da British Cotton Ginnery (BCGA), BATA Shoes, PZ Depot, da Manto Processing Company, lamarin da ya haifar da asarar ayyukan yi da kuma durƙushewar tattalin arziƙi.

British Cotton Ginnery (BCGA), wanda a da yake ɗaya daga cikin manyan masu samar da ayyukan yi a garin Gombe, ya daina aiki gaba ɗaya, har ma da al’umman da ke kewaye da wurin suna ci gaba da alhinin rashin kamfanin.

Ɗaya daga cikin masana’antun da suka durƙushe shi ne ‘Manto Processing Company’ da ke Kumo, Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, wacce aka gina domin sarrafa ruwan mangoro da tumatir. An ƙaddamar da shi ne a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, amma bai yi aiki ko da yini guda ba tun daga lokacin. Duk da haka, gwamnatoci da suka biyo baya ba su nuna wata aniyar farfaɗo da shi ba.

Sauran kamfanonin da suka durƙushe a Gombe sun haɗa da PZ Depot, BATA Shoes Company, da kuma Onigbinde Stores da ke cikin garin Gombe.

Waɗannan kamfanoni a da sun taka muhimmiyar rawa wajen kasuwanci da samar da ayyukan yi, amma matsalolin tsadar gudanar da aiki, sauyin kasuwa, da kuma rashin ingantattun kayayyakin more rayuwa suka tilasta musu rufewa.

Wasu daga cikin mazauna garin, kamar Jafaru Abdullahi, wani dattijo mai shekara 80 a Gombe, sun ɗora alhakin wannan koma-baya kan gazawar gwamnati da kuma rashin damuwar daga ƴan siyasa.

Ya ce: “Akwai dubban matasa marasa aikin yi da za a iya ɗauka aiki, amma kamar yadda nake gani, gwamnati ba ta da niyyar farfaɗo da irin waɗannan masana’antun da nake da tabbacin za su kawo ci gaba a jihar.”

Binciken jaridar LEADERSHIP Sunday ya gano cewa masana’antu da dama a Gombe sun durƙushe ne sakamakon rashin wutar lantarki mai ɗorewa, ƙarancin ƙwararrun ma’aikata, da kuma dogaro kacokan ga shugabannin da suka kafa su. Rashin samar da ingantattun manufofin masana’antu daga gwamnati ya ƙara dagula matsalar.

Arewa

Sai dai kuma, an yi wani ƙoƙarin farfaɗo da masana’antu a jihar. A shekarar 2025 aka ƙaddamar da Premier Seed Processing Factory da ke cikin Muhammadu Buhari Industrial Park, wanda ke bayar da ayyuka na sarrafa iri da kuma shiryawa cikin kwali. Haka zalika, Al-Yuma Fertilizer Plant da ke Kwadon ta samar da ayyuka kai tsaye tare da tallafa wa manufofin noma na jihar.

Duk da haka, ƙoƙarin da aka yi domin jin ta bakin Kwamishinan Harkokin Kasuwanci, Masana’antu da yawon buɗe ido na Jihar Gombe, Nasir Mohammed, ya ci tura har zuwa lokacin da ake wallafa wannan rahoto.

 

SOKOTO

Ragowar tsofaffin masana’antu guda biyu, Sokoto Furniture Factory da Zaki Bottling Company na ci gaba da tunatar da mazauna Jihar Sokoto irin yanayin kasuwanci mai bunƙasa da jihar ta taɓa samu a baya.

Sokoto Furniture Factory, mallakin gwamnatin jihar, da kuma Zaki Bottling Company, mallakin marigayi Alhaji Shehu Malami, sun kasance manyan masu samar da ayyukan yi har zuwa farkon shekarun 1990, lokacin da suka fara durƙushewa.

A da, Furniture Factory ta shahara wajen ƙera kayan ɗaki masu inganci, yayin da Zaki Bottling Company ta kasance ɗaya daga cikin manyan masu samar da lemun kwalba a jihar da ma wajenta.

Durƙushewar Furniture Factory ta samo asali ne daga rashawa da kuma rashin ingantaccen gudanarwa, yayin da durƙushewar Zaki Bottling Company kuwa aka danganta ta da rikicin siyasa tsakanin marigayi Sarkin Musulmi, Alhaji Ibrahim Dasuki, da mai kamfanin.

Har yanzu ba a yi wani ƙoƙari na farfaɗo da waɗannan masana’antun guda biyu ba.

A halin yanzu kuma, sabbin kasuwanci da ke fitowa a jihar sun fi karkata ne ga ƙananan masana’antun ruwan leda (pure water), waɗanda ke da ƙarancin damar bunƙasa.

 

KANO

A Kano, masana’antar African Teɗtile Manufacturer (ATM) ta durƙushe a shekarar 2023 sakamakon tsadar gudanar da aiki da kuma faɗuwar hannun jari.

Shugaban ƙungiyar National Union of Teɗtile, Garment and Tailoring Workers of Nigeria (reshen ATM), Kwamared John Obeikwu, ya bayyana cewa kamfanin ya fara aiki tun 1998 da ma’aikata kusan 3,500.

Kamfanin, wanda K. Akar ya mallaka, yana samar da zanen ƙyalle mai kaso 100 na auduga, amma ya rufe saboda tsadar kayan masarufi, tsadar wutar lantarki, da kuma gasa mai tsanani daga kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasar China.

Obeikwu ya ce tun daga shekarar 2004, yawan ma’aikatan kamfanin ya ragu zuwa kusan 300. Daga bisani aka sayar da shi ga wani sabon mai shi wanda ya yi alƙawarin farfaɗo da kamfanin, amma har yanzu bai fara aiki ba.

Shugaban ɗakin kasuwanci da masana’antu na Kano (KACCIMA), Usman Darma, ya nuna ƙarancin wutar lantarki a matsayin babban ƙalubale, inda ya ce farashin wutar lantarki a Kano ya fi tsada idan aka kwatanta da jihohi irin su Legas da Ogun.

Ya kuma koka kan yawan ribar da bankunan kasuwanci ke ɗorawa, da kuma wahalar da ake samu wajen samun kuɗi daga hukumomin gwamnati.

Yayin da yake kira ga gwamnati da ta samar da yanayi mafi sauƙi ga masana’antu musamman a Arewacin Nijeriya, Usman Darma ya bayyana cewa ɗakin kasuwanci na Kano (KACCIMA) ya jajirce wajen ganin an kammala ayyukan CNG da AKK kafin ƙarshen wannan shekara.

Ya ce: “Da zarar an kammala waɗannan ayyuka, za a ƙara samar da wuta da rarraba ta ga masana’antu da ke Sharada, Bompai, da Challawa, da sauran wurare a cikin jihar, domin ƙara ƙarfin sarrafawa da kuma ƙarfafa sabbin masana’antu.”

 

NASARAWA

A Jihar Nasarawa, masana’antu masu zaman kansu da na gwamnati da dama sun durƙushe sakamakon yanayin kasuwanci mara kyau.

Muhimman kamfanonin masu zaman kansu da aka rufe sun haɗa da Delta Prospectors Limited, mai babbar masana’antar sarrafawa a kan titin Jos, Lafia. An kafa shi a 1995 domin samar da barytes ga kamfanonin mai da iskar gas, amma ya yi aiki na tsawon shekaru biyar kacal.

Wani kamfani kuma, Oil Chem Nigeria Limited, da ke kan titin Makurdi, Lafia, wanda ke ba da ayyukan haƙowa da injiniyan ruwan rijiyoyi, an rufe shi bayan shekara bakwai da fara aiki a 2001.

Daga cikin kamfanonin gwamnati na jiha da suka durƙushe akwai: Fertiliser Blending Plants da ke Lafia da Keffi, Nasarawa Beef Factory da ke Masaka, Nasara Sacks Factory da ke Akwanga (wanda aka kafa a 2002), da kuma Nas Spring Water Company da ke Lafia (wanda aka kafa a 2001).

Wasu daga cikin waɗannan kamfanoni an ba su haya na tsawon shekaru 7 zuwa 10 domin su ci gaba da rayuwa. Sai dai duk da wannan ƙoƙari, Nasara Sacks ya durƙushe.

A ’yan shekarun baya-bayan nan, musamman tun daga 2019, an kafa sabbin kamfanoni da dama. Waɗannan sun haɗa da Olam Nigeria Ltd, Aɓatar New Energy Materials Company Limited, da Ganfeng Lithium Mining Company. Haka kuma, manyan irin su Dangote Sugar Refinery, Azama Nigeria Ltd, da Flour Mills Nigeria sun kafa ofisoshi a jihar.

Ƙoƙarin da aka yi domin jin ta bakin Kwamishinan Harkokin Kasuwanci, Sana’a, Masana’antu da Zuba Jari na Jihar Nasarawa, Mohammed Otto, bai yi nasara ba.

Sai dai wani babban jami’i a ma’aikatar ya bayyana rashin ingancin gudanarwa, tsadar wutar lantarki, da kuma rashin sauƙin samun kuɗin waje (foreɗ) a matsayin manyan matsalolin da ke addabar masana’antu a jihar.

 

KOGI

Kamfanin Tama Da Ƙarafa na Ajaokuta, Ya Shafe Fiye da Shekaru 40 a Durƙushe Kamfanin Tama Da Ƙarafa na ‘Ajaokuta Steel Company’ da ke Jihar Kogi ya shafe sama da shekaru arba’in ba tare da aiki yadda ya kamata ba. Duk da alƙawurran da gwamnatoci daban-daban suka dinga yi, har yanzu aikin farfaɗo da shi bai tabbata ba.

Masu ruwa da tsaki sun jaddada cewa farfaɗo da Ajaokuta na da matuƙar muhimmanci ga dawo da kuzarin tattalin arziƙin Nijeriya, inda suka bayyana cewa rashin kammala shi babban abin takaici ne ga ƙasar.

An kafa kamfanin a shekarar 1979 a ƙarƙashin ma’aikatar wutar lantarki da ƙarafa ta wancan lokaci, tare da hangen nesa na samar da miliyoyin tan na ƙarafa a duk shekara. Wannan wuri da ya mamaye kadada 800, an tsara shi a matakai uku:

Mataki na ɗaya: Samar da tan miliyan 1.3 a shekara. Mataki na biyu: Samar da tan miliyan 2.6 a shekara. Mataki na uku: Samar da tan miliyan 5.2 a shekara.

Duk da cewa an fara aikin tun 1980 kuma aka kai kashi 98 na kammalawa zuwa shekarar 1996, aikin ya tsaya cik tun bayan ficewar kamfanin M/s TPE daga ƙasar Tarayyar Soɓiet (USSR).

Ana ƙiyasta cewa Nijeriya tana cin ƙarafa da ya kai darajar Dala biliyan 3.3 a duk shekara, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin kammala wannan babban shiri.

Tsohon shugaban ƙungiyar ma’aikata, Otori Salihu, ya ɗora laifin durƙushewarsa kan maƙarƙashiyar ƙasashen waje da kuma rashin kishin ƙasa daga wasu ƴan Nijeriya.

Ya ce: “Muna farin cikin ganin babban sauyi a yadda Shugaba Ahmed Bola Tinubu ke tafiyar da al’amarin wannan shimfiɗata ƙarafa.” Tsohon ma’aikaci, Musa Idris, ya ƙara da cewa:

“Banda Shugaba Shehu Shagari, kowace gwamnati sai dai maganganu ne kawai kan burin Ajaokuta. Ku duba yadda rashin aikin yi ya yi yawa. Matasa suna yawo babu wani abin yi.”

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ajaokuta a majalisar tarayya, Hon. Sanni Egidi Abdulraheem, ya jaddada cewa: “Idan aka farfaɗo da Kamfanin Karafa na Ajaokuta, zai tallafa wa gina layin dogo, ya kawo canjin fasaha, gina ƙwarewar ma’aikata, samar da ayyukan yi, rarraba kuɗaɗen shiga, da kuma rage kashe kuɗaɗen waje wajen shigo da ƙarafa daga ƙasashen waje.”

Ya ƙara da cewa: “Ina kira ga Shugaban Ƙasa da kuma Ministanmu su guji shisshigi ga maƙiyan ƙasa waɗanda ke son Nijeriya ta ci gaba da zama kasuwa ta jari-hujja ga ƙarafan waje.”

 

ZAMFARA

In Zamfara State, no fewer than ten industries haɓe been reported to haɓe partially or completely collapsed, while about 7,000 people lost their jobs as a result.

Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gabatar ya nuna cewa durƙushewar waɗannan masana’antu na iya kasancewa yana da alaƙa da Zamanin Dimokuraɗiyya na biyu a 1999.

Haka kuma, an gano cewa Kamfanin Zamfara Teɗtile Industries kaɗai, wanda ya ke ɗaukar ma’aikata kusan 4,000, ya durƙushe a wani ɓangare na shekarar 2003, daga bisani kuma ya sallami kusan kashi 95 cikin ɗari na ma’aikatansa a 2004 domin ci gaba da aiki.

Sauran masana’antu kamar ginneries da sauran kamfanoni, waɗanda a da suke bayar da ayyuka ga dubban mutane, duk sun kulle, abin da ya janyo matsanancin rashin aikin yi a Gusau da sauran ƙananan hukumomi na jihar.

Bisa ga bincike, lokacin da waɗannan masana’antu suke aiki kafin durƙushewarsu, suna ɗaukar ma’aikata tsakanin 300 zuwa 1,000, gwargwadon ƙarfin kowanne.

Haka kuma, an gano cewa wasu daga cikin kamfanonin sun kulle ne saboda ƙarancin wutar lantarki mai ɗorewa, banda wasu da masu su suka shiga siyasa kuma suka zama ƴan siyasa.

LEADERSHIP Sunday ta gano cewa durƙushewar waɗannan masana’antu, wanda ya haifar da asarar ma’aikata ta hanyar sallama da yawa, ya shafi tattalin arziƙin jihar ta hanyar rage samun kuɗaɗen shiga.

Tun bayan durƙushewar waɗannan masana’antu, wasu daga cikinsu sun shafe shekaru 30 har zuwa 50 suna aiki jihar ba ta sake samar da wani kamfani makamanci ba, sai dai ɗaya kaɗai mai suna HAMSTORE Integrated Company Limited, wanda ke ɗauke da ma’aikata kusan 150.

Kamfanin mallakin Hamisu Isah ne, wanda yake a kan hanyar Jaurin Rogo a cikin Ƙaramar Hukumar Gusau ta jihar.

Ga jerin masana’antu da kamfanonin da suka durƙushe a Jihar Zamfara: Zamfara Teɗtile Industries Limited, mallakar haɗin gwiwar masu zuba jari na Ƙasar Sin tare da gwamnatin jiha, dake Gusau Industrial Area.

Gusau Oil Mills, mallakin Janar Aliyu Gusau, ma a Gusau Industrial Area. Gusau Tanning Company Limited, mallakin Alhaji Garba Dakin Gari, dake cikin wannan yankin masana’antu.

Muhammadiyya Metal and Construction Company Limited, mallakin Alhaji Mainasara Mai Gidaje, shima a Gusau Industrial Area. Gusau Sweet Factory Limited, mallakin Jakadan Yuguda Gusau. Gusau Ginnery Company, mallakin Dogon Koli Magami, da kuma wani Gusau Ginnery Company mallakin Ibrahim Mallaha, dukkansu a Gusau Industrial Area.

Mayanchi Ginnery Company, mallakin Alhaji Danfulani Mai Doya, dake kan hanyar Sokoto a Mayanchi. Sahabi Liman Kaura Ginnery Company, mallakin Alhaji Sahabi Liman Kaura a Gusau Industrial Aea. ISMA Ginnery Limited.

Ƙoƙarin LEADERSHIP Sunday na samun ganawa da shugaban Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Zamfara, Kwamared Sani Halliru, da kuma Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu na jiha, ya ci tura, domin ko dai ba a ɗaga wayoyinsu ba ko kuma ba a iya samun layukansu gaba ɗaya.

 

KADUNA

A Jihar Kaduna, tsohuwar ƙayatacciyar cibiyar masana’antar yadi da masana’antu kusan 13, yanzu duk sun durƙushe, lamarin da ya jefa dubban ma’aikata cikin ƙunci.

Daga cikin masana’antun da suka durƙushe akwai: Kaduna Teɗtile Limited (KTL), Arewa Teɗtile, Norteɗ, Finteɗ, United Nigerian Teɗtiles Limited (UNTL) da sauransu.

A gefe guda kuma, masana’antun da har yanzu ke aiki a Kaduna, duk da cewa ba sabbi ba ne sun haɗa da: Olam Feeds and Hatchery, Indomie Noodles, Eurofoam, Mouka Foam da wasu makamantansu.

 

Filato

Ga Jos International Brewery (JIB) kuwa, gwamnatoci da dama sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi fiye da guda uku (MoUs) tare da abokan hulɗa na cikin gida da na waje domin farfaɗo da wannan kamfani mallakin gwamnati da ya durƙushe, amma duk bai haifar da wani sakamako ba.

Jos International Breweries PLC (JIB) tsohon mai sarrafa giya ce ta Rock da Class Lager beer. Tuni dai kamfanin ya kwanta dama na tsawon lokaci. Haka kuma, JIB ta taɓa ƙera Royal Malt, abin sha mai zaƙi da ya yi fice musamman a yankin Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da kuma sassan Jihar Kaduna.

Idan za a tunawa, an kafa JIB ne a shekara ta 1975 a lokacin gwamnatin Joseph Gomwalk, inda BARC farm ta kasance reshe na kamfanin.

A lokacin da kamfanin brewery ɗin na Jos International Breweries (JIB) ke aiki, yana samun mafi yawan kayan masarufi daga BARC farm, wanda hakan ke haifar da manyan kuɗaɗen shiga tare da kafa wasu kamfanoni reshe kamar Pioneer Milling Company.

An sayar da BARC farm ga wani manomi mai zaman kansa fiye da shekaru 20 da suka wuce, kuma a da yana ɗaukar ma’aikata sama da 4,000 ta hanyoyi kai tsaye da ba na kai tsaye ba.

Sai dai shekaru na rashin gudanarwa, watsi da aka yi da shi da kuma satar dukiya sun jefa shi cikin ƙangi.

A halin yanzu, filin Jos International Breweries (JIB) an yi amfani da shi a shekarar da ta gabata ta gwamnatin jihar wajen adana kayan tallafi. A lokacin da wakilinmu ya ziyarci wurin, ba a ga kowa a cikin harabar kamfanin ba.

BARC Farm a da ta kasance ginshiƙin noman zamani, kiwo, da sarrafa kayan gona, tana samun sabuwar rayuwa a shekarar 2025 ƙarƙashin jagorancin sauyi na Gwamna Caleb Mutfwang.

A ranar 29 ga Maris, gwamnatin Jihar Plateau, tare da haɗin gwiwar Plateau Youth Council (PYC) da sauran ƙungiyoyin matasa, ta duba tsararrun gine-ginen gona da suka lalace.

A wani muhimmin mataki, Gwamna Caleb Mutfwang ya miƙa kadada 3,400 na BARC Farms ga matasan Filato, yana basu damar noma ƙasar da samun abin dogaro.

Wannan shiri ya zo ne tare da tallafin gwamnati na Naira biliyan 1 (N1,000,000,000) wanda zai rufe dukkan farashin noma, ciki har da shuka, kayan aikin gona, ayyukan faɗakarwa, tsaro, masauki, da abinci, da sauransu.

 

Arewa Ba Talaka Bace

Ɗan majalisar wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, kwanan nan ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya na da arziki fiye da Kudu.

Sai dai Jibrin ya lura cewa yankin bai yi amfani da albarkatun ɗan’Adam da na ƙasa da ke cikinsa yadda ya kamata ba, sakamakon rabuwar kai da kuma rashin shugabanci nagari.

Ya jaddada cewa Arewacin Nijeriya na da babban damar tattalin arziƙi fiye da Kudu, inda ya kawo hujjoji kamar yawan jama’a, ƙasar gona mai kyau, da kuma yalwar ma’adanai.

Ya ce: “ Ku yarda da ni cewa, Arewacin Nijeriya na da arziki fiye da Kudu. Abin da ya rage shi ne cewa ba mu taɓa samun yanayi da muka yi amfani da duk damar mu ba. Muna da yawan jama’a, muna da ƙasar gona mai kyau, muna da dukkan albarkatun ma’adanai da za ku iya tuna haka.

A kudu abin da ake magana akai shi ne mai da iskar gas kawai; babu wani ma’adanin da za ku iya tunani wanda ba mu da shi a Arewa.”

Jibrin ya yi ƙorafin cewa maimakon amfani da waɗannan albarkatu, fitattun ƴan Arewa sau da yawa suna kawo cikas da kansu a bainar jama’a, abin da ke raunana yankin siyasa da tattalin arziƙi.

Ɗan majalisar ya yi kira ga Arewacin Nijeriya da su haɗa kai, inda ya jaddada cewa daga nan ne kawai za a iya cike damar arziki da tasirin siyasa a Nijeriya.

Masani ya ɗora laifin kan watsi da yin muhimman ayyuka domin dogaro da Mai

A gefe guda, masani kan haraji, Gabriel Olawuyi, ya danganta sakaci da jihohi suke yi wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa ga dogaro da mai da kuma kuɗaɗen da suke samu daga asusun tarayya (federation account).

A cewarsa, jihohi 36 na tarayyar sun samu jimillar kuɗi har Naira tiriliyan 4,103,463,895,991.12 daga asusun tarayya a cikin rabin farko na shekarar 2025, daga watan Janairu zuwa Yuni.

Wannan adadi bai haɗa da kuɗin cikin gida da jihohi suka tara (IGR) ba, ko kuma tallafin gida da na ƙasashen waje daga ƙungiyoyin agaji ba.

Ya ce: “Ga kuɗin da suke zuwa Abuja suna rabawa don kusan babu abin da suka yi. Shi ya sa gwamnoni da dama ba sa damuwa da masana’antu a jihohinsu.”

Daftarin hukuma da jaridar LEADERSHIP Sunday ta samu sun nuna cewa a watan Janairu 2025, duk jihohi an raba musu raba Naiara biliyan 611,974,517,167.65.

Rabon ya ƙaru zuwa Naira biliyan 718,980,039,823.78 a watan Fabrairu, sannan ya ɗan ragu zuwa Naira biliyan 698,237,745,901.35 a watan Maris.

Haka kuma, ya ƙara raguwa zuwa Naira biliyan 663,059,048,511.21 a watan Afrilu, amma ya tashi zuwa Naira biliyan 709,294,748,209.63 a watan Mayu, kafin ya ɗan sauka zuwa Naira biliyan 701,917,796,377.50 a watan Yuni.

In the first siɗ months of the year, inɓestigations by LEADERSHIP Sunday showed that Kano State got N130,561,884,996.12 billion; Kaduna, N102,313,144,368.08 billion; Katsina, N98,001,661,450.71 billion; and Borno, N90,751,737,876.57 billion.

A cikin watanni shida na farkon shekara, binciken LEADERSHIP Sunday ya nuna cewa:

Jihar Kano ta samu Naira biliyan 130,561,884,996.12; Jihar Kaduna ta samu Naira biliyan 102,313,144,368.08; Jihar Katsina ta samu Naira biliyan 98,001,661,450.71; Jihar Borno ta samu Naira biliyan 90,751,737,876.57.

 

Wasu jihohi kuma sun samu kamar haka:

Bauchi: Naira biliyan 91,302,654,057.23; Jigawa: Naira biliyan 89,666,582,459.19; Niger: Naiar biliyan 88,133,126,665.33; Sokoto: Naira biliyan 84,612,635,197.25; Filato: Naiara biliyan 80,135,662,640.41; Kogi: Naira biliyan 82,804,029,930.78; Binuwe: Naiar biliyan 88,267,832,061.80; Kebbi: Naira biliyan 79,954,097,659.22.

A cikin rabin farko na shekarar 2025, wasu jihohi sun samu rabon su kamar haka:

Adamawa: Naira biliyan 79,142,291,194.68; Zamfara: Naira biliyan 77,988,854,173.47; Yobe: Naira biliyan 74,541,528,297.59; Kwara: Naira biliyan 73,329,996,963.66; Gombe: Naira biliyan 72,422,887,970.03; Taraba: Naira biliyan 72,543,126,509.53; Nasarawa: Naira 70,015,932,583.01.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: ArewaMasana'antu
ShareTweetSendShare
Previous Post

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

Related

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12
Manyan Labarai

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

9 hours ago
An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta
Manyan Labarai

An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

13 hours ago
Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi

17 hours ago
An Shirya Haɗin Gwiwa Da Hukumomi Don Magance Matsalar Ambaliyar Ruwa
Manyan Labarai

An Shirya Haɗin Gwiwa Da Hukumomi Don Magance Matsalar Ambaliyar Ruwa

18 hours ago
Majalisar Tarayya Ta Magantu Kan Gawar Da Aka Samu A Harabarta
Manyan Labarai

Majalisar Tarayya Ta Magantu Kan Gawar Da Aka Samu A Harabarta

19 hours ago
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina
Manyan Labarai

Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

22 hours ago

LABARAI MASU NASABA

Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

Rushewar Masa’antu Ya Jefa Al’umma Da Dama Cikin Ƙangin Talauci A Arewacin Nijeriya

September 14, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

September 13, 2025
Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

September 13, 2025
Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

September 13, 2025
An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

September 13, 2025
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

September 13, 2025
An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

September 13, 2025
Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

September 13, 2025
Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

September 13, 2025
Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

September 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.