Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan gidaje 3,813 suka lalace sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a kananan hukumomi 13 da ke Jihar Katsina.
An ruwaito cewa Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar ce ta bayyana haka ranar Litinin.
- Mutane 8 Sun Mutu A Ruwa A Jihar Jigawa
- Magidanci Ya Nemi Matarsa Ta Biya Naira Miliyan 1.6 Kafin Ya Sake Ta A Kaduna
A yayin da yake hira da manema labarai, kakakin hukumar, Malam Umar Muhammad, ya ce mutum uku sun mutu a karamar hukumar Kankara yayin da mutum biyu suka rasu a Mai’adua.
Ya bayyana cewa gwamnatin Jihar tana yin dukkan abin da ya kamata domin ambaliyar ruwa ba ta auku a jihar ba, yana mai cewa an kafa kwamitin gaggawa wajen ganin ba a fuskanci barkewar amai da gudawa ba.
Ya ce: “A Kankara, gidaje 176 sun rushe, a Danja kuma gida je 125 suka lalace, sai kuma Kankia inda gidaje 86 suka rushe, yayin da a birnin Katsina gidaje 620 suka lalace, Musawa 482, Batagarawa 361, Kusada 311 yayin da Sabuwa gidaje 111 suka rushe.
“A Zango, ruwan saman ya lalata gidaje 105, a Batsari, ya rusa gidaje 443, a Funtua gidaje 258 sun rushe, a Safana gidaje 581 sai kuma Ingawa kusan gidaje 154 suka rushe.
“Kazalika gidaje 176 sun rushe yayin da mutum uku suka rasu a ibtila’in a Kankara yayin da gidaje 154 suka lalace a Ingawa.”