Gwamnatin Rwanda da hadin gwiwar kamfanin fasaha na Huawei na kasar Sin, sun kaddamar da sabon shirin dake da nufin bunkasa bayar da horon fasahar zamani a yankunan da suka kasance koma-baya a fadin kasar.
Shirin da ake kira DigiTruck, wani aji ne na tafi-da-gidanka dake amfani da lantarki daga hasken rana, da aka sanya wa kananan kwamfutoci da sadarwar intanet da sauran na’urorin koyo da koyarwa.
An kaddamar da shirin ne ranar Juma’a a makarantar sakandare ta Kagarama dake birnin Kigali, kuma shirin mai wa’adin shekaru 3 zai shafi ‘yan Rwanda 5,000 a fadin gundumomin kasar 30. Haka kuma, zai tallafawa shirin samar da sauyi na kasar na NST2 dake mayar da hankali kan horar da ‘yan kasar miliyan 1 ilimin fasahar zamani. Jami’ai sun bayyana cewa shirin na tafi-da-gidanka zai tabbatar da cewa hatta jama’ar yankuna masu nisa sun samu ilimin fasahar zamani.
Da yake jawabi yayin kaddamarwar, ministan ilimi na kasar Rwanda Joseph Nsengimana ya ce shirin na hadin gwiwa ya nuna kudurin kasar na samar da ilimin fasaha ba tare da barin kowa a baya ba.
Shi ma babban sakataren ma’aikatar kula da fasahar sadarwa da kirkire-kirkire ta kasar, Eraste Rurangwa, cewa ya yi, DigiTruck wani muhimmin bangare ne na shirin Rwanda na One Million Coders, wanda wani jigo ne dake ingiza cikar burin kasar na zama mai bunkasa tattalin arziki bisa dogaro da ilimi. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp