Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (wadda a yanzu ake kira Nigeria Revenue Service — NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa sabbin dokokin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2026.
Adedeji ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Alhamis, bayan da shugaban ƙasa ya amince da sabbin dokokin gyaran haraji guda huɗu.
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara
- Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga
Ya ce wannan mataki babban ci gaba ne domin ƙirƙirar tsarin haraji na gaskiya, da kuma inganci.
Ya ce an tsara a bar tazarar watanni shida tsakanin sa hannun shugaban ƙasa da kuma lokacin da za a fara amfani da dokokin, domin a samu lokacin wayar da kai, da gyaran hukumomi don aiwatar da su yadda ya kamata.
Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi shi ne sauya sunan hukumar daga FIRS zuwa Nigeria Revenue Service (NRS).
Adedeji ya ce har zuwa sa’o’i biyu kafin sanarwar, sunan hukumar shi ne FIRS, amma yanzu sunan ya koma NRS.
Ya bayyana cewa sabuwar hukumar ba za ta tsaya kan tattara haraji kawai ba, domin yanzu tana damar tattara sauran kuɗaɗen shiga da ba na haraji ba.
Hakazalika, za ta yi aiki cikin ’yanci tare da bin ƙa’idojin bayyanan aiki da bin diddigin nasarori.
Ya ƙara da cewa sabuwar hukumar za ta mayar da hankali sosai wajen cimma nasarori, kuma za ta yi aiki da ƙwarewa kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya.
Shi ma shugaban kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa ko da kuwa doka na da kyau, idan ba a aiwatar da ita yadda ya kamata ba, ba za ta amfanar da ƙasa ba.
Ya ce yanzu shugaban ƙasa ya umarce su da su fara aiki yadda ya kamata.
Oyedele ya ja hankalin jama’a cewa wannan gyara ba zai yi nasara ba sai kowa ya bayar da gudunmawarsa.
Ya ce gwamnati kaɗai ba za ta iya aiwatar da wannan sauyi ba.
Dole ne a samu haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki, ƙungiyoyin fararen hula, ƙwararru, da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa.
Shugaba Tinubu tun da farko ya ce dokokin harajin an tsara su ne don gina ƙasa, tare da kawar da ɓarna da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.
Wannan gyaran haraji yana cikin babban shirin gwamnatinsa da ke neman kyautata yanayin kasuwanci, ƙara samun kuɗaɗen shiga, da kuma ganin ci gaba ya waanzu a faɗin ƙasar.
Yanzu da aka sa ranar fara amfani da dokokin a Janairun 2026, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki suna da lokaci don shirya duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa sabbin dokokin harajin sun cika burinsu na kawo ci gaba ga ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp