A Jihar Zamfara, wani bincike ya nuna yadda ‘yan bindiga ke tilasta wa mazauna wasu garuruwa biyan haraji don samun damar rayuwa ba tare da kai musu hari ba.
Binciken wanda jaridar Daily Trust, ta gudanar ya nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankunan.
- Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Titi Da Gadar Sama Ta Huɗu A Borno
- Inganta Kiwon Lafiya: Gwamna Buni Ya Ziyarci Sashen Koyar Da Kwararrun Likitoci A Damaturu
Wannan lamari ya jefa mutane cikin tsananin fargaba da matsin tattalin arziƙi.
Rahoton ya nuna cewa tun daga watan Janairun 2025 zuwa yanzu, al’ummar yankunan sun riga sun biya kimanin Naira miliyan 500 ga ƙungiyoyin ‘yan bindiga domin tsira da rayukansu.
A cikin watan Janairu kaɗai, jagoran ‘yan bindiga da aka kashe, Isuhu Yellow, ya ƙaƙaba wa mutane harajin Naira miliyan 172.7 a kan ƙauyuka 25 tare da tilasta musu ba da kayan amfanin gona.
Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.7.
Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe.
A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60.
Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu a Gama Lafiya, an ƙaƙaba wa yankin harajin Naira miliyan 10.
Haka kuma, haraji ya ci gaba da yaɗuwa a Unguwar Tofa (Naira miliyan 26.6), Makera (Naira miliyan 15), Sungawa (Naira miliyan 20), Rakyabu (Naira miliyan 7), Yalwa (Naira miliyan 8), Mai Saje (Naira miliyan 11), da Langa-Langa (Naira miliyan 20 zuwa 30).
Sauran yankunan da ‘yan bindigar suka ƙaƙaba wa haraji sun haɗa da Gidan Dawa, Rijiyar Tsakar Dawa, Dan Jibga da kuma Bilbis. Malam Ibrahim Maru, wani mazaunin karamar hukumar Maru, ya ce matsalar ta’addanci a yankin na ƙara ta’azzara fiye da da.
Lamarin na nuna irin ƙalubalen da jama’a ke fuskanta a hannun masu aikata laifuka, wanda ke buƙatar kulawar gaggawa daga gwamnati da hukumomin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp