Biyo bayan wani sabon harin kunar bakin wake da ake zargin yan ta’addan Boko Haram da kitsa shi a Gwoza dake jihar Borno ta hanyar amfani da yara mata, ‘Yan Nijeriya sun shiga fargaba a yankin Arewa Maso Yamma har ma da sauran sassan Nijeriya.
Akalla zuwa lokacin hada wannan rahoto, an tabbatar da mutuwar 30 tare da raunata wasu da dama da wata majiya ta ce sun kai 41 sakamakon raunuka daban-daban da suka samu a harin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mata ne sanye da jigidar bama-bamai suka kutsa kai cikin taron jama’a, a lokacin bikin daurin aure a garin na Gwazo inda suka tayar da abubuwan na fashewa.
Hare-haren dai sun sake cusa fargaba da tsoro a zukatan ‘Yan Nijeriya musamman na yankin da abin ya faru saboda yadda aka samu kusan tsawon shekara biyar ba tare da an fuskanci harin na kunar bakin wake ba.
Jama’a sun tuna irin ukubar da suka sha a yayin da ake kokarin dakile hare-haren kunar bakin waken a baya, ta hanyar sanya dokoki da suka hana walwala da girke shingayen bincike na sojoji da rashin aminci da yarda da juna a tsakanin al’umma da sauran abubuwa da dama na takurar rayuwa.
Mahangar Masana Kan Lamarin
Wasu daga cikin masana harkokin tsaro da suka tofa albarkacin bakinsu ga manema labarai sun bayyana cewa lallai wadannan sabbin hare-hare kira ne na kara mikewa haikan a kan yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro domin yayin da ake zaton bako ya tafi, yana nan bayan gari.
Daya daga cikinsu, Dakta Kabiru Adamu, ya nunar da cewa abin da ya faru ya nuna akwai matsala daga bangaren tattara bayanan sirri wanda ya zama wajibi a gano abin tare da magancewa.
Ya bayar da shawarar cewa, idan ana so a yi riga-kafi, a farad aga kan wannan abin da ya faru kar a je da nisa, “a binciko su wanene ne suka yi, su waye suka kitsa sannan da binciko yadda abin ya faru. Daga wannan zai zama an kashe maciji tare da sare kansa”. Ya bayyana.
Shi kuwa wani Babban Kwamandan Sojin Sama mai ritaya, Musa Salmanu, ya bayyana ra’ayinsa ne da cewa, kar gwamnati ta yi tunanin amfani da zallar karfi wajen magance sabuwar matsalar, inda ya bukaci sake yaukaka zumuncin aiki a tsakanin dakaru da al’ummomin yankunan da rashin tsaron ya ki ci ya ki cinyewa.
Haka nan ya bukaci karfafa sarakuna domin samun nasarar da ta dace, kasancewar har yanzu sarakuna suna da tasiri sosai a cikin al’ummomin yankunansu.
Bugu da kari, Group Captain Sadeek Shehu wanda ya bayyana cewa harin kunar bakin wake na karshe da aka gani kafin wannan shi ne wanda ya auku a Konduga a shekarar 2019, ya ce, watakila wannan sabon yunkurin na ‘yan ta’adda manuniya ce a kan yadda ruwa ya kare wa dan kada amma sai suke kokarin nuna wa duniya cewa har yanzu da sauran rina a kaba.
Ya yi kiran rubanya kwazon aiki a tsakanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa an yi hanzarin dakile sabuwar barazanar tare da riga-kafin sake komawa baya, kamar yadda abubuwa suka rincabe bayan kai harin farko na bom a shalkwatar ‘yansanda ta kasa da ke Abuja a ranar 16 ga watan Yunin 2011.
Nijeriya Ba Za Ta Sake Komawa Cikin Firgici Ba – Tinubu
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu wanda ya aike da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima zuwa Gwoza domin jajanta wa al’umma abin da ya faru kwana biyu da kai hare-haren, ya lashi kaifin takobin cewa wadanda suka kai harin za su dandana kudarsu.
Shugaban ya bayyana harin a matsayin sakamakon matsin lambar da sojoji suke wa ‘yan ta’adda a yankunan da ake yakarsu.
Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta dauki karin matakai na kiyaye rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa kan ya ba da tabbacin za su ci gaba da rubanya kwazonsu har sai sun ga bayan masu hana kasa zaman lafiya baki daya.
Kar A Sake Mayar Da Arewa Maso Gabas Fagen Wasan Kwaikwayon Ta’addanci – Atiku
Da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan koma-baya da aka samu a fannin matsalar tsaro, biyo bayan wannan hari na kunar bakin wake, tsahon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya mayar wa da Gwamnatin Tarayya martanin cewa kar ta mayar da Arewa Maso Gabas filin baje kolin salwantar da rayukan al’umma ta fuskar ta’addanci.
Atiku ya yi Allah wadai da wannan harin na bam yana mai gargadin gwamnatin tarayya da ka da ta mayar da yankin tamkar gidan wasan kwaikwayon ta’addanci.
Ya bukaci a kara kaimi wajen yin aiki yadda ya kamata, kana kuma ya zargi gwamnatin da rashin tabuka abin a zo a gani wajen yin tsayin daka domin tallafa wa jami’an tsaro wajen samun nasarorin yaki da ayyukan ta’addanci.
“Wannan abin bakin-ciki ne a ce duk da nasarorin da jami’in tsaro suka samu a baya, amma har yanzu munanan ayyukan ta’addanci na so su sake kunno kai a kasar nan, bai dace ba sam a ce wadannan ‘yan ta’adda su sake tada zaune tsaye a yankin Arewa maso Gabas.”
“Mun yi Allah wadai da wannan mummunan harin da wasu yan kunar bakin wake suka kai wajen taron bikin aure, kana da wajen yin jana’iza, hadi da kuma asibiti a ranar Asabar.
“Wannan koma-baya ne kuma abin takaici ne dangane da yadda kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ke kokarin dawo da ayyukan ta’addanci sabo, kuma wannan yana zuwa ne sakamakon rashin gwamnatin da ta san ciwon kanta, wadda ta kasa yin tsayin daka wajen kare kasa da ‘yan kasa.
“Bisa ga wannan, ya zama dole mu yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a bisa wuyanta wajen tabbatar da cewa yankin Arewa maso Gabas bai koma cikin filin wasan kwaikwayon ayyukan ta’addanci da tashin hankali ba.” In ji Atiku.
Majalisar Wakilai Ta Tafka Muhawara
A nasu bangaren, ‘yan majalisar wakilai sun bukaci a gudanar da bincike na musamman kan wadannan tashin bama-bamai da suka faru a jihar Borno tare da dora zargin faruwar al’amarin kan jami’an tsaro.
Majalisar ta kuma umarci kwamitinta mai kula da harkokin tsaro da leken asiri na kasa cewa ya binciki hare-haren tare da kawo mata cikakken rahoto cikin makonni biyu masu zuwa.
Da yake gabatar da bayanai a kan lamarin yayin tafka muhawa a majalisar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Damboa/Gwoza/Chibok a Jihar Borno, Ahmed Jaha, ya ce wadannan hare-haren kunar bakin wake da aka kai Jihar Borno a baya-bayan nan sun faru ne sakamakon yi wa harkokin yaki da ta’addanci rikon sakainar kashi tare da rashin gamsuwar al’umma da hukumomin tsaro a kasar nan.
Ya kara da cewa hare-haren baya-bayan nan sun faru ne sakamakon irin yadda jama’a da jami’an tsaro suka kashe jiki tare da yadda zukatansu suka riya musu cewa an zo karshen matsalolin tsaro, yanayin da ya bai wa ‘yan ta’addan damar aiwatar da mugun nufinsu lokacin da aka daina daukar matakan riga-kafi.
“Ba za mu zura ido a ci gaba da yi wa harkokin tsaro ko-in-kula ba. Saboda ko shakka babu rashin gamsuwar da ya dabaibaye zukatan al’umma dangane da jami’in tsaro yana daya daga cikin dalilan da suka sa wannan abu ya faru a mazabata,” In ji shi.
Hon. Jaha ya ce bai kamata a ce an kyale ‘yan kunar bakin wake suna cin karensu babu babbaka ba, saboda kawai sun yi shigar tufafi iri daya da sauran jama’a ba.
“Ina so mu sani cewa al’ummar gari sun gano fuskokin wadannan ‘yan kunar bakin waken, kuma an gano cewa ‘yan ta’adda ne suka dauke su aiki, bayan da suka goge musu tunani tare da saka musu mummunan nufi, sannan aka shigo da su Gwoza daga wani wuri domin su haddasa wannan aika-aika.
“Sun shigo cikin wata shiga ta musamman kuma kala- kala, saboda haka muna kiran jama’a a farka; idan ka ga mutum- namiji ko mace, yaro ko babba a cikin wata shiga wadda ba ka gamsu da ita ba, ka kai rahoto, lallai a kara kula sosai.
“Akwai matukar bukatar jami’an tsaro su kara kaimi wajen fito da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri tare da hada kai da al’ummomin da matsalolin tsaro suka shafa domin dakile hana afkuwar irin wadannan munanan hare-haren kunar bakin wake a nan gaba.
“Saboda bangaren ayyukan jami’an tsaron leken asiri wani muhimmin al’amari ne wajen yaki da ta’addanci, kuma yana da matukar muhimmanci ga jami’an tsaro, wanda shi ne babban guzirin kayan aiki kuma jigon da zai bayar da goyon bayan da suka dace domin tattara bayanan sirri masu inganci cikin lokaci, don dakile kai hare-hare kafin faruwar su.”
Da yake bayar da gudunmawa, a muhawarar majalisar, Hon. Abdussamad Dasuki, ya ce dole ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki mataki kan ministocin tsaro, mashawarci kan harkokin tsaro da makamantansu.
Ya ce da yawa daga cikinsu sun kasa tabuka abin da ya dace wajen kare rayukan ‘yan kasa da dukiyoyinsu.
Ya ce, “Wadannan mutanen da aka dora wa alhakin kula da harkokin tsaron kasar nan sun kasa a ma’aunin da aka dora su a kai. Saboda a kowace rana, bayanan da ke fitowa daga yankuna daban-daban a fadin kasar nan, ana asarar rayukan ‘yan Nijeriya. Lokaci ya yi da za mu fito da kudurin da zai taka wa matsalolin nan birki.”
“Ina ganin sama da kashi 50 cikin 100 na kudurorin Majalisar Wakilai zango na 10 da ta zartar da su na da alaka da tsaro. Saboda haka bari mu nemo bangaren da yake da laifi. Muna da kwamitoci kan fannin tsaro, za mu so su bincika wannan, domin na san za su iya kallon wadanda ba su yi abin da ya dace ba, kuma su ne ya kamata a dora wa laifin abubuwan da suke wakana.” In ji shi.
A nasa martanin, shugaban kwamitin tsaro a zauren Majalisar, Babajimi Benson ya ce mafita kawai ita ce a bai wa rundunar ‘Yansandan Nijeriya fifiko a fannin ayyukan tsaron cikin gida.
Ya kara da cewa, “ya kamata a yi amfani da dukkan dabarun da suka dace wajen amfanin da al’umma wajen gano makarkashiya irin wannan kafin su faru.
“Sakamakon haka ne a kowane lokaci ina bayar da shawarar cewa kwamitin ya duba kundin tsarin mulkin kasar nan dangane cewa ya kamata ya bai wa ‘Yansandan jihohi fifiko.
“Saboda mafi yawan al’ummar da muke da su a kasar nan ya ninninka adadin yawan jami’an tsaron da muke bukata.” Ya nanata.
Sauran wadanda suka yi magana a kan wannan kudirin sun hada da Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa na Nijeriya, Yusuf Gagdi tare da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Idris Wase.
Shalkwatar Tsaro Ta Mayar Da Martani
A kakkausan martanin da Shalkwatar Tsaro ta Kasa (DHK) ta mayar wa da ‘yan ta’addan da suka kitsa wadannan hare-haren kunar bakin waken, ta ce kwanakin da suka rage musu a duniya ‘yan kalilan ne, tare da shan alwashin kawo karshen wannan rashin tsaro, wanda ta ce ba za ta gushe ba cikin damarar hana masu tayar da kayar baya cin karensu ba babbaka a duk inda su ka buya.
A wata sanarwar Manema Labaru mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarun shalkwatar,Manjo Janar Edward Buba, shalkwatar ta bayyana wasu ayyukan da Rundunar Sojojin Nijeriya ta aiwatar a baya-bayan nan wanda ta ce ya basu nasarar halaka yan ta’adda da dama tare da lalata makaman da suke amfani da su, inda hakan ya rage tasirinsu da karfinsu.
Jami’in hulda da jama’ar ya ce wannan harin kunar bakin wake da ‘yan ta’adda suka kai na tsoro ne a kan jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba, don su nuna wa duniya cewa har yanzu suna nan da karfinsu tare da kokarin rufe rauni da koma-bayan da suke samu bisa farmakin da muke kai musu.
“Sun yi haka ne don ‘Yan Nijeriya su zata cewa suna nan da karfinsu. Amma mu mun san cewa wannan salo ne da ‘yan ta’adda suke amfani da shi domin boye gaskiyar abubuwan da suke fuskanta na magagin karshen al’amarin su.”
“Sojojin Nijeriya suna sane cewa, ‘yan ta’addam taliyar karshen rayuwarsu suke ci, saboda ga dukkan wadanda suka san ‘yan ta’addan, sun san suna da dabarun aiwatar da abin da zai ja hankalin jama’a, don kawai su karkatar da hankalin jama’a da sanyaya gwiwar ‘yan kasa ko sanya shakku bisa goyon bayan da jama’a suke bai wa rundunar Sojojin Nijeriya da kokarin Gwamnatin Tarayya na kawo karshen matsalolin tsaro.”
“Saboda haka, muna kira ga ‘Yan Nijeriya su tashi tsaye, su kasance cikin taka-tsan-tsan, su ci gaba da bayar da goyon baya ga kokarin da rundunar sojin Nijeriya ke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, wajen murkushe ta’addanci da ‘yan ta’adda a fadin Nijeriya.”
“Bugu da kari kuma, wannan yunkuri da yan ta’adda suke yi wajen kai sabbin hare-haren da yake tayar da hankalin jama’a na gajere lokaci ne domin sojoji ba za su daina kai musu zafafan farmakin ba a duk inda suka buya.” In ji shi.
Manjo Buba ya bayyana cewa dakarun hadin gwiwa na Operation Hadin Kai ba kanwar lasa ba ne a yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, saboda a kowace rana a bakin daga suke tare da kai jerin hare-hare ga yan ta’adda a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar Borno baki daya.