Yayin da gwamnatin Amurka mai ci ke kara tsaurara matakan shiga kasar ga baki daga ketare a matakai daban daban, masharhanta na ta bayyana baiken wadannan matakai, wadanda ko shakka babu ba za su haifarwa Amurkan, da ma sauran sassan kasa da kasa ‘da mai ido ba.
A baya bayan nan, mun ga yadda gwamnatin Amurkan ta sanar da cewa baki masu shiga kasar sai sun yi wata rajista ta daban, baya ga biza da suke dauke da ita. Kazalika, tun daga 8 ga watan Yunin nan ta haramtawa al’ummun kasashen Afghanistan, da Myanmar, da Chadi, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da Equatorial Guinea, da Eritrea, da Haiti, da Iran, da Libya, da Somalia, da Sudan da Yemen damar shiga kasar bisa “wai” dalilai na tsaron kasa.
- Bukola Saraki Ya Tallafawa Al’ummar Mokwa Da Gudunmawar Kuɗi
- Trump Ya Umarci A Bincika Lafiyar Ƙwaƙwalwar Tsohon Shugaban Ƙasa Biden Yayin Mulkinsa
Wadannan matakai, kari ne kan yunkurin da gwamnatin Amurkan ta yi na dakile ikon jami’ar Harvard, na baiwa dalibai da masu zuwa ayyukan bincike damar shiga jamiar. Inda har aka jiyo wasu rahotanni na cewa ma’aikatar tsaron kasar na nazari kan bizar daukacin ’yan kasashen waje wadanda ke da alaka da jami’ar ba wai dalibai kadai ba.
Kafin hakan, gwamnatin Amurka ta ayyana manufar soke damar jami’ar Harvard din ta daukar dalibai daga ketare, da rage kudaden da gwamnatin kasar ke samarwa jami’ar, matakin da wata kotun kasar ta bayyana da haramtacce. Wadannan matakai dukkaninsu na nuni ga yadda gwamnatin Amurka mai ci ke kokarin siyasantar da harkar ilimi, da halastattun hakkokin matafiya na kasa da kasa bisa fakewa da batun tsaron kasa, duk kuwa da cewa ba wasu shaidu na hakika dake nuna wajibcin daukar wadannan matakai.
Alal hakika, bai kamata musayar ilimi, ko hadin gwiwar gudanar da bincike su zama makamin siyasa ba. A hannu guda, tauyewa matafiya damar zirga-zirga tsakanin kasashen duniya ciki har da Amurka, mataki ne na keta hakkokin al’ummun duniya, wanda hakan ke kara fayyace gibin dake akwai, tsakanin kalaman Amurka na fatar baki, da kuma ikirarin da take yawan yi na “wai” tana martaba ’yancin bil adama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp