Da yawa masu sha’awar kallon fina finan da ake shiryawa a masana’antar Kannywood sun saba gani ko jin ana amfanin da harshen Hausa wajen isar da duk wani sako da fim din yake dauke dashi, ba kasafai aka saba ganin fina finan da ake shiryawa a masana’antar Kannywood sun fito da wani yare na daban ba illa Hausa.
Amma kuma daya daga cikin Hausawa da suka kware a turancin Ingilishi kuma furodusan fina-finai a masana’antar Kannywood Kabiru Musa Jammaje ya dukufa wajen ganin ya canza wannan tunani da mutane ke yi na cewa masana’antar Kannywood bata da wata hanyar isar da sako sai ta hanyar harshen uwa (Hausa).
- Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda
- Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
Inda a shekarar 2010 ya fara tunanin fara shirya fina finai da za a dauka a arewacin Nijeriya amma kuma a yi magana da yaren Ingilishi, wanda a tunaninsa zai sa sakon da fim din zai isar ya isa zuwa sauran sassan Duniya, ma’ana ba ya tsaya a iya inda ake jin harshen Hausa ba ya tafi zuwa ga wata al’ummar da ke jin yaren Ingilishi.
A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga gida ta NOUN inda na karanci ‘Education Administration and Planning’.
Jammaje ya ci gaba da cewa a yawace yawacen da na yi na tafi kasashe irinsu Afirika Ta Kudu da kasar Kenya inda a wancan lokacin sai na lura cewa mutanen wadannan kasashen biyu suna yi wa duk wani dan Nijeriya wani kallo na daban sakamakon abin da suka ga ana nunawa a wasu fina finan da suke kallo da ake shiryawa a kudancin Nijeriya (Nollywood, ganin ana nuna abubuwa kamar tsafe-tsafe, fashi da makami, damfara ko kuma mutane masu shan jini.
Hakan yasa suke yi wa duk wani da ya zo daga Nijeriya irin wannan kallon, wannan sai ya ja hankalina na ce to mi zai hana mu da muke yin fina-finai da babu duk wadannan abubuwa marasa kyau a cikinsu a nan Arewacin Nijeriya (Kannywood) mu kawo masu namu fina-finan su kalla, sai kuma naga cewar babu wata hanya da hakan za ta iya faruwa sai idan wadannan mutane za su ji abin da muke fadi a fina-finan.
Wannan ne ya kara mani kwarin gwuiwar tunkarar wannan aiki gadan-gadan, sai na tuntubi wasu daga cikin abokaina da ke a masana’antar kamar su Falalu Dorayi, Abba El Mustapha da sauransu domin zakulo hanyoyin da za su kaimu ga samun nasara, kuma Alhamdulillahi hakan ya matukar tasiri domin kuwa abin da muke yi a yanzu ya samu karbuwa a ciki da wajen Nijeriya in ji Jammaje.
Jammaje wanda yanzu haka yake da makarantun koyar da harshen Turanci a mafi yawancin jihohin Arewacin Nijeriya ya ci gaba da cewa, a lokacin da na shigo masana’antar Kannywood ban yi tunanin bayan Ali Nuhu akwai wadanda suke jin turanci ba, amma kuma bayan na shiga sai na gano akwai wadanda su ka kware sosai a turanci a masana’antar wanda hakan sai ya sau kaka mana aikin.
Da yake amsa tambaya a kan wace irin nasara ya samu tun bayan fara wannan yunkurin Kabiru Musa Jammaje ya ce akwai tarin nasarori da aka samu, domin kuwa a shekarar 2017 a wata ziyara da ya kai kasar Ingila akwai wasu iyali da ya nuna masu fim din There Is A Way, sai suke mamaki har suna tambaya dama akwai wani yanki da ake kira Arewa a Nijeriya, sai suke cewa basu taba jin wani yare wai Hausa ba, sai na ce masu ai wannan fim fin kacokan dinsa an yi shi ne a arewacin Nijeriya kuma duka abin da suka gani shi ne asalin abin da bahaushe ya kunsa, kama daga zamantakewa, al’ada da kuma yanayin sutura sai suka dinga mamaki.
Sannan kuma fina finan da muka yi sun samu daukaka sosai don kuwa har da kyautuka muka dinga samu a ta sanadiyarsu kamar fim din ‘In Search Of The King’ da ya taba lashe kyautar Fim Mafi Kyawu a wani bikin karramawa da aka yi, sai kuma sabon fim dinmu mai suna Nanjala wanda yanzu haka akwai wani wurin yawon bude ido da ke kasar Turkey da suka saye fim din domin su nunawa bakinsu (Tourist) irin yadda al’adar mutanen kasashen Afirika musamman Arewacin Nijeriya ta ke.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp