Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu domin jama’ar jihar Ribas su tarbi zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tarba mai kayartawa.
Zababben shugaban kasar, a yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da zai yi a jihar Ribas, zai kaddamar da gadar Rumuola/Rumuokwuta da babbar kotun Majistare ta Fatakwal a ranakun Laraba da Alhamis.
Wike, a wani labarai a jihar a ranar Talata, ya ce yayin ziyarar yakin neman zaben shugaban kasa da Tinubu ya kai jihar Ribas, na nuna sha’awar bawa Tinubu damar kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar bayan babban zabe.
Wike ya ce, an aikewa da zababben shugaban kasa takardar gayyata bayan kammala babban zabe, wanda kuma shugaban ya amsa gayyatar cikin yardarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp