A lokutan baya kadan da suka wuce, mafi yawan mutanen na yi wa fina-finan Hausa kallon masu basira guda daya, wato basirar soyayya zalla, ba tare da fadada basirarsu zuwa ga abubuwan da ke damun al’umma domin shawo kan matsalar har a magance ta.
Sai dai kuma akasari a fina-finan Hausan da ke fita a yanzu masu dogon zango, na zuwa ne da sabon salon da ke birge al’umma na abin da ya shafi rayuwar yau da kullum, ciki kuma akan taba kowanne bangare domin fadakarwa, nishadantarwa, gami da wa’azantarwa.
- Sojoji Sun Cafke ‘Yan Bindiga 7, Sun Kubutar Da Wasu Mutane
- Ko Kananan Sana’o’i Na Biya Wa ‘Yan Nijeriya Bukatunsu?
Hakan ne ya faru ga sabon fim din da ke shirin fita a makon nan mai suna JAMILA. Wanda HAFSAT SA’EED ta dauki nauyin shiryawa.
Fim din ya tattara abubuwan da ke wakana a wannan lokaci, wanda suka addabi al’umma na rayuwar yau da kullum, Wakilyarmu RABI’AT SIDI BALA Ta ji ta bakin Jarumar da ta shirya fim din tare da bayanan wasu jaruman da suka taka rawa cikin shirin na JAMILA, ga dai tattaunawar haka:
Masu karatu za su so jin cikakken sunanki?
Sunana Hafsat Sa’eed amma an fi kirana da Momy.
Akwai sabon fim mai suna Jamila, wanda ke kika shirya, me ya ja hankalinki har kika shirya wannan fim din?
Masha Allah! na dade ina harkar fim kuma tun da na shigeta nake sha’awar zama ‘Producer’ wato me shiryawa, Allah bai sa zan zama ba sai a yanzu.
Me fim din yake kunshe da shi?
Darussa daban-daban
musamman a kan wannan yanayin rayuwar da muke ciki a yanzu.
A kan me aka yi fim din?
Masha Allah! mun yi shi a kan halin da ake ciki yanzu, game da yadda ake dauke-dauken mutane wato ‘kidnappings’.
Kamar wadanne Jarumai ne suka taka rawa cikin fim din, kuma wacece Jarumar?
Ni ce da kaina na ja fim din sai Lawan Ahmad da Ummi ibro da Abba El-Mustapha da Darakto Ibrahim Bala da dai sauransu.
Kamar tsawon wanne lokaci kuka shafe kuna daukar shi wannan fim na Jamila?
Ba mu dade sosai muna daukar fim din ba gaskiya, satin nan muka kammala ‘season one’ domin Darakto yana da kokari, in ya sa abu a gaba musamman kan aikinshi wanda a gaskiya da wani Darakto din ne sai mun fi wannan lokacin.
Shi wannan fim na Jamila me dogon zango ne ko kuwa takaitaccen labari ne?
Me dogon zango ne, A yanzu mun gama ‘season one’.
Yaushe za a saki fim din, ko kuwa ya fita?
A’a! Bai fita ba, ana gab da fara sakin tallarshi cikin satinnan in sha Allah.
A ina za a iya samun fim din, ko kuwa za a rinka haskawa a wasu gidajen Talabijin ne?
Alkhausar Hausa Tv da ke YouTube, sai kuma tashar Dadin kowa a Startimes.
Ya kike kallon yadda karbuwar fim din zai kasance ga su masu kallon?
To a yanzu haka ma masoya nata tambaya ta yaushe zai fito. Gaskiya ina ji a jikina in sha Allah zai karbu sosai.
Ko akwai wasu matsaloli ko kalubale da kuka fuskanta wajen daukar shi wannan fim din?
Gaskiya babu wata matsala da muka fuskanta, komai ya tafi yadda ake bukata, sai dai mu ce Alhamdulillah.
Bayanan Wasu Daga Jaruman Fim din JAMILA, Ibrahim Bala (Darakta):
Ni ne mai Bada Umarni cikin shirin, kuma na fito matsayin Abokin Lawan Ahmad.
‘JAMILA’; Shiri ne da aka yi shi akan abubuwan da suke faruwa a wannan zamani na rashin gaskiya da rashin gane yadda rayuwa take ciki, Lawan Ahmad ya auri wata sabuwar jaruma mai tasowa Hafsa ya kammala karatu babu aiki ita kuma iyayenta na da karfi, sai ta matsa akan gadonta dake hannun yayanta Abba Elmustapha akan a bashi ya ja Jari saboda halin da yake ciki cewa zai je Abuja neman aiki, ita kuma tana tsoron hanyar da rashin tsaro, karshe dai aka nemi miji aka rasa sakamakon rasa kudin da mijin zai ja jari a hanyar zuwa Abuja. Ana zargin mutum uku na farko Abba ElMustapha, na biyu Ibrahim Bala abokinsa, na uku shi kansa Lawan Ahmad mijn nata. Shirin Jamila muna da kyakkyawar fatan zai karbu a duniya, saboda yayi dai-dai da abun da yake faruwa a wannan zamani da kuma jajirtattun ma’aikatan da jaruma da mukai aiki da su.
Abin da ya fi bani wahala wajen daukar fim din Jamila; na farko zirga-zirga da guraren da akai ta yawon daukar shirin.
Rabi’atu Sani Umar (Ummi Ibro):
Sunana Rabi’atu Sani Umar wadda aka fi sani da Ummi Ibro. Rawar dana taka a fim din JAMILA ni dai kawar Jamila ce, Aminiyarta wadda ba ta boye min komai na sirrinta, walau na farin ciki ko kuma akasin hakan. Masha Allah fim din in sha Allah zai je inda ma bamu zata ba, Abin da ya ban wuya a wajen daukar fim din Jamila, To kin san ita rayuwa kowanne abu a ciki akwai kalubale, to inda sabo an saba, ko ya baka wuya ma ba lallai ya dame ka ba.
A b u b a k a r Sadeek Fulani (A.S Fulani):
Sunana Abubakar Sadeek Fulani ana kirana da (A.S Fulani), na taka rawa a fim din Jamila matsayin Najib kanin Sabit wanda shi ne mijin JAMILA. Sabit dai Yayana ne cikin shirin, wanda yayi karatu har zuwa matakin ‘Digree’ amma bai samu aiki ba, ni Najib dan makaranta ne, kuma ni kadai ne kaninsa a cikin gidanmu, a kokarin Sabit na ganin ya samu aiki a kayi kidnapped dinsa, har ta kai ga jami’an tsaro suna tuhuma ta da cewa da sa hannuna aka sace Yayana Sabit, dan haka aka kamani aka kulle ni, kuma ni ne abokin shawarar Jamila matar yayana Sabit a cikin fim din.
Abin da ya bani wahala shi ne; ta bangaren ‘Director’ saboda ganin cewar wannan fim babban fim ne to duk abun da ya zo a rubuce sai an yi shi yadda yake, hakika na ji dadin hakan sosai, saboda shi burinsa ya ga na yi abin da zai burge masu kallo, shi yasa duk abin da nayi ba dai-dai ba sai yayi min fada, sannan ya gyramin har ta kai shi ma ransa yana baci da yin gyaran. Hakika wannan fim babban fim ne domin, zai kayatar da masu kallo, kuma zai bayar da darasi ciki sosai, sai dai na ce masu kallo ku hanzarta ku nema da zarar ya fita.