Sabon kamfanin jiragen sama na Riyadh, mallakar asusun zuba jari na mahukuntan Saudiyya na yin duba yiwuwar sayen kimanin jiragen sama samfurin Boeing, daga 300 zuwa zuwa 400.
A makon da ya gabata, kafar yada labarai ta Bloomberg ta ruwaito cewa, kamfanin kera jiragen sama na Boeing Co BA.N na shirin sayar da akalla jiragen sama guda 150 ga sabon kamfanin jiragen sama na Riyadh.
- APC Ta Yi Allah Wadai Da Rusau Din Da Abba Ke Yi A Kano
- Gwamnan Zamfara Ya Ziyarci NADDC, Ya Nemi Hadin Gwiwar Bai Wa Matasan Jihar Horo
Sai dai, kamfanin kera jiragen sama na Boeing, bai fitar da wata sanarwa kan hakan ba.
Kazalika, shi ma sabon kamfanin jiragen sama na Riyadh, bai yi bayani kan bukatar da kafar yada labarai ta Reuters ta tura masa na neman karin bayani ba.
A kwanan baya ne kamfanin na Boeing ya kara samun wata bukatar son jiragen sama guda 78 zuwa guda 787 daga gun hukumar Jiragen sama ta Saudiyya da kuma wata bukatar daga wajen sabon kamfanin jragen sama na Riyadh.