Sabon kwamishinan Ƴansandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya fara aiki a hukumance tare da yin alƙawarin tabbatar da ingantaccen tsaro a fadin jihar. A yayin bikin bankwana da aka gudanar a Bompai domin karrama tsohon kwamishinan Ƴansanda, Husani Gumel, CP mai barin gado ya nuna godiya ga jami’ai da rundunar Ƴansandan jihar Kano bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin zamansa, inda ya danganta hakan ga nasarar da ya samu.
An bayar da kyautuka a yayin bikin mai ƙayatarwa, ciki har da lambar yabo mai kyau daga ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya reshen jihar Kano, tare da nuna godiyar da tsohon CP ya yi. Bikin ya kuma karrama jami’an Ƴansanda, da masu hannu da shuni kan ƙoƙarin da suke yi na samar da zaman lafiya a jihar.
- Gwamnan Kano Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Kawo Karshen Fadan Daba A Kano
- An Ɗage Shari’ar Da Gwamnatin Kano Ta Kai Aminu Ado Zuwa 2 Watan Yuni
A nasa jawabin, AIG Gumel ya buƙaci ci gaba da ba wa sabon CP goyon baya, inda ya jaddada mahimmancin haɗin gwuiwa don cimma manufofin da aka sanya a gaba na wanzar da zaman lafiya da tsaro a Kano.
Tabbas sabon kwamishinan yana da aiki na a gabansa duba da yadda gwamnati da hukumar ke zaman doya da manja ga kuma rikicin daba da ya sake kunno kai jihar. Haka kuma ga rikicin masarauta ana ta fama da shi ga kuma masu kwacen waya.