• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Kwamitin Lura Da Takara Da Sin Da Amurka Ta Kafa Ba Zai Haifar Da Dan Mai Ido Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

A ’yan kwanakin nan, majalissar wakilan Amurka ta kafa wani kwamiti da ta ce zai lura da batutuwa masu nasaba da takarar da kasar ke yi da kasar Sin, har ma majalissar na ganin kwamitin zai iya zama wata garkuwa, da abun da ya kira hanyoyi mabanbanta da Sin ke zama barazana ga Amurka.

Duk da cewa aikin da aka dorawa kwamitin bai wuce na bincike da kuma ba da shawara ba, kafa shi wata manuniya ce ga kudurin siyasar Amurka, na nacewa tunanin cacar baka tsakanin ta da Sin.

  • Sin Ta Tallafawa Makarantun Sudan Ta Kudu Da Litattafai Sama Da 300,000

Masharhanta da dama na ganin an kafa kwamitin ne domin karfafa matakan gwamnatin Amurka mai ci na dakile kasar Sin, karkashin amincewar majalissar dokokin kasar, da goyon bayan gwamnatin shugaba Joe Biden, wanda ko shakka babu cikin tsawon lokaci, tasirin hakan zai ci gaba da illata alakar Sin da Amurka.

Idan mun waiwayi tarihi, za mu ga bayan aukuwar harin 11 ga watan Satumban 2001, Amurka ta mayar da batun yaki da ta’addanci sahun gaba, a manufofinta na tsaro da diflomasiyyar kasashen waje. Daga bisani kuma a shekarar 2017, gwamnatin tsohon shugaban kasar Donald Trump ta bullo da abun da ta kira matakan tsaron kasa, wanda karkashin hakan ta ayyana kasar Sin a matsayin “Muhimmiyar abokiyar takara” ga Amurka. Tun daga wannan lokacin ne kuma, Amurka ke ci gaba da bunkasa wannan manufa ta fuskoki daban daban.

To sai dai abun tambaya a nan shi ne, tun daga waccan manufa ta tsaron kasa, wadda karkashinta Amurka ta rika yakar kasashe daban daban, tare da haifar da mummunan tasirin yaki kan miliyoyin fararen hula, har zuwa dokar ayyana Sin a matsayin barazana ga Amurka, wacce manufa ce a cikin su ta haifarwa Amurka wani alfanu?

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Sanin kowa ne cewa, manufar Amurka ta yake-yake, da daura damarar yin takara maras adalci, ko rarraba kan yankunan duniya zuwa rukunoni, da maida wasu sassa saniyar ware, ba abun da suka haifarwa kasar sai koma baya, da kara jefa al’ummun duniya cikin mummunan yanayi.

Don haka dai ya kamata Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta yi watsi da manufofin wariya da nuna kyama, ko yunkurin dakile kasar Sin ta dukkanin fannoni, kafin hakan ya kai ga haifar da mummunan sakamako da zai jefa Amurka cikin halin matsin tattalin arziki, tare da gurgunta alaka da moriyar sassan biyu. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
CBN Da ‘Yansanda Za Su Sa Kafar Wando Daya Da Masu Sayar Da Sabbin  Kudi    

CBN Da 'Yansanda Za Su Sa Kafar Wando Daya Da Masu Sayar Da Sabbin  Kudi   

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.