A kokarin da jami’an tsaro a Jihar Kaduna suke yi wajen magance ayyukan ‘yan ta’adda a fadin jihar, a karon farko kwamandan rundunar sojoji ta daya da ke jihar Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya jagoranci wata tawaga na jami’an soja domin kai farmaki a sansanin ‘yan ta’adda da ke garuruwa Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello da kuma Dogon Dawa duk shiyyar karamar hukumar Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
Tawagar sun tarwatsa sansanin ‘yan ta’addan, inda suka kwato bindiga kirar AK47 da babura guda 18 da dunkulen harsashi na musamman guda 27 da kuma jikkata ‘yan ta’addan masu yawan gaske.
Hakazalika, tawagan sun ceto wasu mutane uku da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a wani kauye mai suna Manini da ke Kan hanyar Birnin Gwari.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya raba wa manema labarai a Kaduna a ranar Litinin 30 ga watan Augustan 2022, ya ce bayan wani taho-mu-gama da sojojin suka yi da ‘yan ta’adda a dajin Birnin Gwari, sojoji sun jikkata ‘yan ta’adda da dama yayin da suka arce suka bar makamansu, lamarin da ya sanya suka kwato bindigogi da babura da kuma kubutar da mutane uku daga hannunsu.
A cewar rundunar sojan, sun kaddamar da kai samamen ne wuraran da ‘yan ta’addan suka yi sansani bisa jagoranci kwamadan rundunar, Manjo Janar Taoreed, tun daga ranar Alhamis na makon jiya har zuwa ranar Litinin na wannan makon, domin tabbatar da cewa an samu saukin kai hare-haren ‘yan ta’addan a Jihar Kaduna.
Rundunar sojan ta bukaci al’ummar jihar musamman ma’aikatan kiwon lafiya da su sanya ido a kan duk wani mutum da zai zo neman agaji bisa samun rauni da ya yi, domin sanar da hukumomin tsaro