A halin yanzu kungiyoyin dalibai da na matasa sun fara gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da kuma nuna bukatar su na a gaggauta ceto dalibai ‘yan mata na Jami’o’in Gwamnatin Tarayya da ke Gusau da Dutsimma wadanda ‘yan ta’adda suka sace. Zanga-zangar da ake gudana a kafafen sadarwa na zamani (Soshiyal Mediya), yana samun karbuwa, don har wasu Jaruman masana’antar Kannywood kamar Ali Nuhu sun shiga tare da nuna goyon bayansu a kan bukatar a kawo karshen sace-sacen dalibai a manyan makarantu. Wannan gangami yana neman ya yi kama da salon da wasu kungoyi suka dauka shekarun baya a lokacin da aka sace dalibai mata na makarantar sakandari n agarin Chibok da ke Jihar Borno (#birngbackourgirls) wanda ya samu karbwa a sassan duniya ciki har da Shugaba Amurka na wanncan lokacin, Barak Obama.
Wannan yana nuna harzukar da matasa suka a yankin arewa a kan haren-haren ‘yan ta’addan a mayan makarantu. Don ko a ranar Laraba tun bayan da ‘yan bindiga suka shiga dakunan kwanan dalibai mata na jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau Jihar Zamfara, gwamnatin jihar da jami’an tsaro suke ta fadi tashin ganin an ceto dukkan wadanda aka sace.
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Kama Kwale-kwale Da Muggan Kwayoyin Miliyan N200 A Legas
- Kazakhstan, Kasa Marar Ruwa Mafi Girma A Duniya, Tana Da Nata Hanyar Shiga Teku
Gwamna Jihar a Dauda Lawal ya a ta bakin mai magana da yawunsa, Alhaji Sulaiman Bala Idris, ya ce, gwamnatin jihar na ba jami’an tsaro dukkan goyon bayan da suke bukata na ganin an ceto daliban a cikin koshin lafiya. Wannan ne ma ya haifar da takaddama a tsakanikn gwamnatin jihar da jami’an gwamnatin tarayya inda ake zargin wasu jami’an gwamnatin tarayya na gudanar da tattaunawar sulhu da ‘yan ta’adda ba tare da sanin gwamnatin jihar ba, abin da gwamnatin tarayya da karyata.
Bayan kwashe awanni muna tattaunawa kan harkar tsaro, a yau na kaddamar da kwamitin da zai fara aiki don samar da Rundunar Kare Garuruwa (Community Protection Guard).
Wannan yana daga cikin shirinmu don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Zamfara.
Babban aikin wannan kwamiti shi ne samar da tsari wanda da shi za a kafa wannan rundunar ta CPG, don mu iya ba da kariya ga garuruwanmu baki daya.
Aiki ne babba, amma da yardar Allah za mu yi nasara.
Babu gudu, ba ja da baya a kudurinmu na kawo karshen ‘yan bindiga. A dalilin haka nake sake nanata cewa ba za mu yi sulhu da mabarnata ba.
A na cikin jamamin sace daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya na Gusau ne sai kuma gashi ranar Laraba 4 ga watan Oktoba 2023 a ka samu labarin sace wasu dalibai mata 5 a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-ma ta Jihar Katsina.
Bayanai sun tabbatar da cewa, an sace daliban ne daga dakuna kwanan su da ke ‘Mariamoh Ajiri Memorial International School’ da misalin karfe 2:30 na daren Laraba, jami’in watsa labarai na rundunar ‘yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadik Aliyu, ya tabbatar da labarin ya kuma ce an samu nasarar kama wasu da ake zargi da hannu a sace daliban kuma a na ci gaba da gudanar da bincike don sanin yadda za a ceto su.
Wannan tashin hankalin ya sa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu umarci jami’an tsaro su gaggauuta ceto sauran daliban da suke hannun ‘yan ta’addan ba tare da bata lokaci ba, bayan an samu nasarar ceto dalibai 7 a samamamen da ‘yansanda suka yi a cikin daji, musamman ganin jami’ar mallakin gamnatin tarayya ne.
Jami’in watsa labaran shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya yi tir da sace ‘yan matan, yana mai kara da cewa, babu wani dalili na sace yaran, wanda laifin su klawai shi ne na kokarin zuwa makartanta neman ilimi.
Shugaban kasar ya mika jajensa ga iyalai da ‘yanuwan daliban, yana mai tabbatar musu da cewa, gwamnati za ta tabbatar da cetosu tare da dawo da su a cikin iyalansu cikin koshin lafiya.
Tinubu ya kuma yi alkawarin tabbatar da tsaro a dukkan manyan makarantun kasar nan, don dukkan ‘yan kasa su damar samun ingantaccen ilimi a fadin tarayya kasar nan.
Wannan barazana ne ga ilijmin mata
Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta bayyana yadda ake sace-sacen dalibai ‘yan mata a manyan makarantumu a mastayin barazana ga kokarin ilimantar da yara mata a arewacin Nijeriya.
Sun bukaci gwamnatin tarayya ta hada kan rundunonin tsaron kasar nan don fito da sabbin hanyoyin kare makarantunmu daga wannan matsalar wanda yake neman zama babbar barazana ga ci gaban yankin arewa da ma Nijeriya gaba daya.
ACF ta bayyana haka ne a takardar sanarwar da sakatarenta na kasa, Farfesa Tukur Muhammad Baba ya sanya wa hannu, ya kuma kara da cewa, ya kamata gwamnati ta yi dukkan kokarin da ya kamata na ganin an ceto daliban ba tare da wani cutarwa ba.
Sanarwar ta kuma kara dacewa, “ACF ta yi tir da wannnan lamarin da kakkausar murya musamman ganin wannan ba shi ba ne na farko a yankin arewa ba kuma wani abu ne da ya kamata a tir da shi a dukka fadin duniya.
“Lamarin yana tayar da hankali ne musamman ganin yana iya durkushe kokarin da ake yi na karfafa harkar ilimin mata a Nijeriya, wanda dama yana fuskantar manyan matsaloli a ‘yan shekarun nan.
“Wannan yana da tayar da hankali in aka lura da yadda wasu iyaye suke shirin janye yaransu mata daga manyan makarantu da yadda wasu ke canza shirin su na zabar wasu jami’o’i saboda yadda yankin ke fuskantar matsalar tsaro.”
Haka kuma shugabban kungiyar ‘Amnesty Int’I reshen Nijeriya,
Isa Sanusi, ya nemi a gudanar da cikakken bincike a kan yadda aka sace daliban Jami’ar Gusau da kuma sauran sace-sacen ‘yan mata a manyan makarantun yankin arewa gaba daya. Ya kuma nemi a dauki dukkan matakai na shari’a don ganin an ceto yaran ba tare da bata lokaci ba.
Sanusi ya kuma kara da cewa, “Ya kamata makarantu su zama waje mai aminci bai kamata su fuskanci barazana da tashin hankali ba a yayin da suke neman ilimi. Jami’an gwamnati sun bayyana cewa, sun shawwo kan matsalar tsaro a yankin arewa amma ayyukan ‘yan ta’adda yana nuna cewa kamar labarin ba haka yake ba.”
“Hari tare da sace dalkibain a jami’o’in gwamnatin tarayya na Gusau wani babban laifi ne da ya shafi kasa da kasa yana kuma neman kawo cikas ga akokarin bayar da ilimi wanda hakki ne ga dukkan bil’adam.
“Daga dukkan alamu hukumomi basu dauki darasin da ya kamata ba a yadda ake sace dalibai a makarantu a sassan yankin arewa, wannan sace-sacen da ake yi na baya bayan yana nuna cewa, ba a yi wani tsari ba na kare dalibai daga wannan annobar na sace daliba da kuma kare aukuwar irin haka a gaba.
“Dole gwamnatin Nijeriya ta gudanar da binicike na musamman don hukunta duk wani da ke da sakaci a faruwar wannan lamarin.