Tsawon lokacin da ‘yan Nijeriya suke dakon jiran fara aikin kamfanin jiragen saman Nijeriya da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya alkawaranta, lamarin ya zama bambara-kwai, yayin da sabon shugaban kamfanin ya yi tonan silili a wannan mako.
Shugaban kafanin jiragen saman Nijeriya, Kaftin Dayo Olumide ya shaida wa kwamitin majalisar dattawa mai kula da hidimar sufurin jiragen sama cewa, jirgin da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar a kwanakin baya da cewa mallakan Nijeriya, zancen ba haka yake ba, domin hayarsu aka dauko daga kasar Habasha (Ethiopia) kwanaki kadan aka sauya masu launi da rubuta sunan ‘Nigeria Air’ da tambarin kasar a jiki domin a yaudari ‘yan Nijeriya da masu ruwa da tsaki.
- Zuba Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku Da Japan Ke Shirin Yi Zai Illata Duk Fadin Duniya
- Cire Tallafin Mai: Tinubu Ya Gana Da Manyan Dillalan Fetur, Ya Ba Da Umarnin Kawo Dauki
Ya ce idan Nijeriya za ta tafiyar da ragamar jirgi, dole ne kayan aikinsa su kasance masu rajista da Nijeriya, kuma sai an samu lasisi da izinin gudanarwa da sauran abubuwan da suke akwai. Ya tabbatar wa duniya da cewa jirgin da aka ce mallakin Nijeriya ne aronsa aka dauko na ‘yan kwanaki kuma tunin aka mayar wa masu shi da kayansu.
Yadda Zancen Ya Faro
A ‘yan awanni da ba su zarce 72 da gwamnatin Buhari ta kammala wa’adinta, gwamnatin kasar ta kaddamar da jirgin na Nijeriya a cibiyar zirga-zirgan jiragen sama da ke filin sauka da tashi na Nnamdi Azikiewe da ke Abuja.
A jawabinsa a wajen kaddamarwar, tsohon Ministan sufuri, Hadi Sirika, ya ce da kyakkyawar hadin guiwa tsakanin kamfanin sufurin jiragen kasar Habasha (Ethiopia) da ake son sayar wa Nijeriya babban jirgin, hakan zai kara kyautata alakar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
“Wannan daya ne daga cikin abubuwan da aka rasa a bangaren sufurin jirage a Nijeriya, jirgin ya yi daidai da matakin kasuwanci da ake da shi a Nijeriya. A zahiri, muna bukatar irin wannan jirgin don haka mun rattaba masa suna ‘Nigeria Air Limited’.”
Ya ce tun shekarar 2016, aka fara yunkurin mallakar jirgin amma sai a wannan karon aka samu cimmawa, “Don haka jirgin zai kasance a nan kuma za mu fara jigila daidai yadda za mu iya yi,” a fadin Sirika.
Mafi yawan al’ummar Nijeriya sun shiga farin ciki da murna da jin an samu jirgin sama mallakin kasar, inda suka yi fatan hakan zai kawo saukin wasu lamuran, sai dai kash.
Ta Ina Gizo Ke Saka: Shugaban Kamfanin Ya Fayyace Zare Da Abawa
Shugaban kamfanin jirgin saman Nijeriya, Kaftin Dayo Olumide, ya shaida cewa, jirgin hadakar da aka kaddamar a Nijeriya bai da rajista. Ya ce an dauko jirgin ne daga kasar Habasha (Ethiopia) a matsayin wanda zai yi ‘yan kwanaki kuma da an kammala abun da ake son yi da shi aka dauka a mayar can.
Ya kara da cewa Nijeriya tana da lasisi din mallakar filayen jirgin sama ne kawai daya daga cikin izini guda biyu da ake bukata kafin gudanar da harkokin sufuri. Ya ce kasar ba ta da izinin fara gudanar da harkokin kasuwanci da jiragen, balle har ya zo a ce ta samu jirginta da za ta fara gudanar da harkokin kasuwanci da shi.
Ya kara da cewa, “Zan fara ba ka amsar tambayarka kafin na ci gaba. Jirgin da aka kawo ya kuma koma inda ya fito, domin hayarsa aka dauko.
“Dukkanmu a nan idan muna da bikin aure a Senegal, za mu iya daukar hanyar jirgi. Ba ka da bukatar sai ka nemi izinin yin hakan, kawai hayar jirgin za ka yi, kuma jirgin za ka biya kudinsa ne, zai zo nan take kuma har ka kwashi fasinjarka ka yi tafiyarka.
“Wannan shi ne abun da muka yi. Amma a kan wannan lamarin aka kaddamar. Tun 2018, duk abun da kuka gani da sunan jirgin mallakin Nijeriya kawai a hoto ne, zane ne ba jirgi ne na hakika ba, amma ina tunanin lokaci ya yi da za mu fara nuna yadda jirgin gaske zai kasance. Kuna gani muna da masu zuba hannun jari, za su iya zuba kudinsu na tsawon shekara 10 zuwa 15. Don haka suna da bukatar a nuna musu hakikanin yadda ake son jirgin ya kasance.
“Don haka mun kawo don mu nuna musu jirgin da yadda ake son ya kasance. Daga nan kuma sai yanayin social media ya shigo ciki.
“Wannan jirgin da ake magana a kai na da rajista ne da Ethiopia. Me ya sa zai kasance mai rajista da Ethiopia? Idan Nijeriya za ta tafiyar da ragamar jirginta, dole ne ya kasance jirgin na dauke da rajistan Nijeriya na ranar 5 ga Nuwamba. Amma jirgin baya dauke da rajistan 5 ga watan Nuwamba saboda hayarsa aka dauko na ‘yan kwanaki kuma da ya kammala ya koma abunsa.
“Idan muka son mu samun lasisin wanda aiki na ne, dole ne mu yi wasu abubuwan, daga ciki dole ne ya zama muna da jirage akalla uku kafin NCA ta ba mu lasisi, sannan dukkanin wadannan jiragen dole ne su kasance masu rajistan Nijeriya.
“Akwai matakai guda biyar da mutum zai bi kafin ya samu lasisi. Mun doshi mataki na daya da na biyu, amma matsalar da muke fuskanta shi ne, idan ka canza abun da muke kira ‘post holders’, wani bangaren kwararru ne da ke hada daraktan kulawa, babban matukin jirgi, idan ka canza su da wasu gaba daya, to ka sake komawa baya kan shirinka, sai an sake musu tambayoyi domin cika ka’idojin hukumar. Ko da yake, sake komawa bayan ba yana nunin ka yi wani abu na kuskure ba ne, hakan gyara ne a tsarin da ake bi.
“Don haka, lokacin da aka kawo wannan jirgin a matsayin na haya, kawai sai kowa da kowa ya kama cewa mun kaddamar da jirgin Nijeriya.”
‘Yan Majalisa Sun Nuna Damuwarsu
A bangarensu, shugaban kwamitin na majalisar dattawan, Sanata Biodun Olujimi da Sanata Smart Adeyemi sun ce, wannan abun takaici ne yadda kokonto da wasiwasi ya shiga cikin lamarin aikin samar da jirgin Nijeriya.
Kazalika, a yayin zaman, ‘yan majalisan sun yi tir da matakan da aka bi, sun misalta hakan a matsayin damfara da zamba.
Nnolim Nnaji ya nuna damuwar bayan da manyan masu ruwa da tsaki a Nijeriya da kamfanin jiragen Ethiopian suka nuna cewa ba su da masaniya kan kaddamar da jirgin da aka ce an yi a Nijeriya kwanakin baya.
Ma’aikatar sufuri ta yi ikirarin cewa Nijeriya ta nuna jirgin ne kawai amma ba kaddamarwa ba.
Mambobin kwamitin majalisar sun nuna bacin ransu da damuwarsu ne lokacin da hukumar kula da sararin samanin Nijeriya (NAMA) ta ce jirgin da aka makala masa launin Nijeriya hayarsa aka yi zuwa Nijeriya.
Wasu da suka kaddamar da maganar NAMA din, sun ce ana iya sauya launin jirgin da Nijeriya ta dauko hayarsa zuwa kowani irin launi da ake so.