Bisa ta’azzarar matsalar tsaro a ‘yan kwanakin nan musamman a Babban Birnin Tarayya Abuja, dakarun Nijeriya sun yi sabon yunkuri domin murkushe barazanar da ake fuskanta musamman a cikin birnin da garuruwan da ke kewaye.
Majiyoyi daga rundunar soji sun shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, tun bayan harin da ‘yan bindiga suka kai wa Dogarawan Shugaban kasa ta ‘Guards Brigade’ kwanakin baya ya sanya rundunar sojin fadada ayyukansu na tsaro zuwa jihohin Neja, Nasarawa da Kogi domin kare babban birnin tarayyar daga hareharen ‘yan ta’adda.
Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta, ta cigaba da cewa, sojojin suna kan farmakar ‘yan ta’adda a sansanonin da suka boye suna kai wa sojoji hare-hare da muhallan gwamnati.
Ta ba da tabbacin cewa dabarun da jami’an tsaro ke amfani da su a yanzu tabbas za su haifar da da mai ido domin kuwa sojoji suna samun nasarori sosai a kan ‘yan ta’addan tare da lalata musu shirye-shiryensu tun daga can maboyarsu, inda zuwa yanzu an kashe ‘yan ta’adda da dama kuma an kamo wasu.
Wakilinmu ya nakalto cewa an shiga zullumi a yankin Abuja a kan matsalar tsaro bayan wasu jerin manyan hare-hare guda uku na ‘yan ta’adda da suka auku.
Na farko shi ne kai hari gidan yarin Kuje wanda hakan ya kai ga tserewar fursunoni daban-daban ciki har da manyan ‘yan ta’adda 63 na kungiyar Boko Haram. Sai kuma harin da aka kai wa dogarawan shugaban kasa a Bwari inda maharan suka kashe wasu sojoji.
Bayan nan sun kuma kai hari ga shingen binciken sojoji da ke ‘Zuma Rock’ a kan iyakar Abuja da Jihar Neja wanda ya janyo jikkatar wasu sojoji, wadannan hare-haren sun jefa mazauna Abuja cikin firgici.
‘Yan ta’addan a wani faifayin bidiyo da suka sake, sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sace Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da wasu fitattun ‘yan siyasa.
Domin kawo karshen matsalolin na tsaro, a halin yanzu rundunar sojin saman Nijeriya ta fara amfani da jiragen yaki samfurin A-29 Super Tucano da gwamnatin tarayya ta sayo su tun a watan Disambar shekarar 2018 amma suka shigo Nijeriya a watan Agustan 2021.
Kwangilar samar da jiragen tsakanin Gwamnatin Nijeriya da ta kasar Amurka ta kai Dala miliyan 500 da zimmar taimaka wa rundunar sojin saman Nijeriya wajen kawo karshen matsalolin tsaro musamman ‘yan ta’addan Boko Haram.
Shekara guda kenan da yin jigilar jiragen amma wasu na ganin an takura wa gwamnatin kasar da ka da ta yi amfani da jiragen kan ‘yan ta’addan inda su kuma ‘yan Boko Haram da mayakan ISWAP da na Ansaru da kuma ‘yan bindiga ke ci gaba da tsula tsiyarsu na ayyukan ta’addanci.
Rashin amfani da jiragen a shiyyar arewa maso gabas, da kuma arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da kuma a ‘yan kwanakin nan maida hankali a Birnin Tarayya Abuja ya bai wa ‘yan ta’addan damar ci gaba da kai hare-hare.
A lokacin da aka tuntubi darakta yada labarai na rundunar sojin sama (NAF), Air Cdre Edward Gabkwet, ya ce, yanzu haka sun fara amfani da jiragen yakin na Tucano amma dai bai ba da cikakken bayani kan hakan ba.
Ya ce, bayyana wuraren da jiragen ke aiki a yanzu ba zai taimake su ba, don haka dai ya tabbatar da cewa jiragen suna kan kokarinsu na dakile aniyar ‘yan ta’adda.
Kazalika, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Sanata Bala Ibn Na’Allah, a ranar Lahadi ya jinjina wa rundunar soji bisa fara amfani da jiragen yakin Super Tucano tare da irin nasaroroin da ake samu sakamakon amfani da su a halin yanzu wajen yaki da matsalar tsaro a kasar nan.
Ya bukaci rundunar sojin saman da ta ci gaba da kara kaimi kan wannan kokarin nata domin ganin an kawo karshen matsalolin tsaro da suka zama ruwan dare a kasar nan.
Ya kuma ce, samar da kayan aikin da suka dace ga dakaru abu ne da ya kamata gwamnati ta kara maida hankali a kai domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Sufeto Janar Ya kara Yawan ‘Yan Sanda A Abuja
Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, IGP Usman Baba, ya tura karin jami’an ‘yansanda a cikin birnin tarayya Abuja domin tabbatar da kare mazauna birnin daga barazanar tsaro da ke addabar su a ‘yan kwanakin nan, tare da basu tabbacin cewa jami’an za su ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyar jama’an birnin.
Shugaban na ‘yansanda ya kuma umarci mataimakinsa mai kula da sashin ayyuka, DIG Bala Zama Senchi, da ya tabbatar da sanya ido a kan jami’an da aka tura domin tabbatar da suna ba da cikakkiyar kariya a yankin Abuja tare da jihohin da ke makwaftaka da ita.
Kazalika ya gargadi mazauna birnin dangane da yada labarun kanzun kurege da ka iya kara rurata matsaloli a maimakon taimaka wa jami’an tsaro.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa, CSP Olumuyiwa Adejobi ya kara da cewa, shugaban ‘yan sandan ya kuma bai wa ‘yan Nijeriya da mazauna Abuja tabbacin cewa za su ci gaba da kokarin kare rayukansu da dukiyarsu tare da dakile aniyar ‘yan ta’adda.
Sannan, ya kara da neman hadin kan ‘yan Nijeriya da samar wa ‘yan sanda bayanan sirri domin taimaka musu wajen kawar da batagari a cikin kasar nan.
Shugaba Buhari Ya Roki Tallafin kasashen Waje Kan Matsalar Tsaro
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yaba wa kasashen waje bisa yadda suke tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar duniya ciki kuwa har da Nijeriya.
Ya bukaci a kara samar da karin hadin guiwa a tsakani kasashe domin kawar da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.
Da yake amsar wasika daga hannun babban wakilin kasar Kanada a Nijeriya, Ambasada James Kingston Christoff da Jakadan kasar Medico a Nijeriya, Juan Alfred Miranda Oritz, Shugaba Buhari ya fada wa jakadun cewa, an samu cimma muhimman nasarori ta hanyar yin aikin hadin guiwa tsakanin kasashe musamman a kan iyakoki, don haka akwai bukatar a kara azama a wannan fannin domin cimma nasarori masu tarin yawa.
Kakakin shugaban kasan, Mista Femi Adesina, a wata sanarwar da ya fitar shekaran jiya ya kara da cewa, “Duniya tana fama da matsalar tsaro da kuma na dumamar yanayi da kuma fama da aka yi da annobar Korona da suka janyo nakasu ga tattalin arzikin duniya, kasashe na ta yunkurin farfadowa daga wadannan matsalolin.
“Fadar da ke ci gaba da faruwa tsakanin kasashen Russia da Ukraine
ta haifar da nakasun wajen daidaito da matsalolin kasahe ke fuskanta, yayin da matsalar tsaro da ke faruwa a Libya ya kara janyo matsalar tsaro a yankunan Sahel tare da janyo nakasu ga dorewar demokradiyya a kasashen Afrika ta tsakiya da ta yamma.
“Nijeriya ma ba a barta a baya ba, muna ta fama da yaki da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, rikicin manoma da makiyaya, da matsalar ‘yan ta’adda. Muna cimma nasarori ta hanyar hadin guiwa na kawance da kasashe irin naku na tabbata da gudunmawar da ake bayarwa za a kawo karshen wadannan matsalolin,” in ji shi.
Shugaba Buhari ya kara da cewa kasashen da suke karkashin kungiyar ECOWAS na hadin guiwa wajen magance matsalolin tsaro da rigingimun na kan iyakoki da sauran matsalolin da suke jibge kama daga na ‘yan ta’adda, safaran mutane ta barauniyar hanyoyi, safaran miyagun kwayoyi, garkuwa da mutane da sauransu.
“Na yi imani matsalar tsaro ya zama batun da ya shafi kowace kasa kuma a shirye kowace kasa take domin shawo kan hakan lamarin. Don haka
akwai bukatar kasashe su kara hadin guiwa da taimakon Nijeriya domin kawo karshen matsalolin tsaron nan da muke fama da su.”
Kazalika, Buhari ya yi amfani da wannan damar wajen neman kasashen wajen da su sanya ido kan zabukan da Nijeriya za ta gudanar a 2023 domin tabbatar da an yi zabuka masu cike da gaskiya da adalci kuma sahihi.
Daga bisani ya nemi Jakadun su dora a kan nasarorin da wadannan suka gada suka cimmar domin kyautata alakar kasashen.
Da ya ke jawabin godiya a madadin Jakadun, babban wakilin kasar Kanada, ya gode wa shugaba Buhari bisa amsar wasikar da suka kawo masa na jakadanci a Nijeriya.
Sun kuma ba shi tabbacin yin ayyukan hadaka domin cigaban kasashen.
Sannan, a shekaran jiya, Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin ta’addanci na bayabayan nan ya shafa a jihohin Sokoto, Kaduna da Filato.
Shugaban ta cikin sanarwar da hadiminsa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta taimaki jihohin wajen shawo kan matsalolin da suke akwai, “Mun bai wa hukumomin tsaro cikakken ikon gudanar da aikin babu sani ko sabo kan ‘yan ta’addan. Na yi tir da hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai wa a sassan kasar nan. Ina jajanta wa iyalan wadanda suka mutu tare da fatan Allah bai wa wadanda suka jikkata lafiya,” in ji shi.
‘Yan Ta’adda Sun Sako karin Wasu Fasinjojin Jirgin kasan Kaduna 5
Wasu karin mutum biyar daga cikin fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Maris sun shaki iskar ‘yanci a tsakiyar makon nan.
Wadanda aka sake din sun hada da Farfesa Mustapha Umar Imam, wanda Likita ne a asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Dan Fodio (UDUS), Sakkwato.
Sauran kuma su ne Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu Sidi and Aminu Sharif.
Mal Tukur Mamu, mawallafin jaridar ‘Desert Herald’ wanda ya taimaka wajen sulhu tsakanin gwamnati da masu garkuwa da mutanen ne ya tabbatar da sake mutum biyar din.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa fasinjojin jirgin kasan Kaduna su 63 ne aka yi garkuwa da su inda aka kashe mutum 9 daga cikinsu.
Ko a kwanakin baya ma dai masu garkuwan sun saki wani rukuni daga cikin wadanda suka yi garkuwa ciki har da manajan bankin noma tare da wasu mutum 11.
Inda zuwa yanzu aka saki mutum 24 daga cikin fasinjojin. Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto dai Har yanzu dai zuwa yanzu sama da mutum 30 na hannun masu garkuwan.
Majalisa Ta Yi Ganawar Sirri Da Manyan Hafsoshi
A halin da ake ciki kuma Majalisar Dattawa ta yi wata ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri na tsaro bisa barazanar tsaron da ake fuskanta.
Shugaban majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya jagoranci sauran shugabannin majalisar wajen gudanar da taron.
Yayin da shi kuma Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro, Janar Lucky Irabo ya jagoranci shugabannin rundunonin tsaron zuwa taron.
A jawabinsa na bude taron kafin su shiga ganawar ta sirri, Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa majalisar ta nuna dukufa sosai kamar takwararta sashen zartarwa wajen ware makudan kudi da amincewa da shi domin ganin an shawo kan matsalar tsaron da ta kawo wa kowa iya wuya, yana mai cewa shi ya sa suka kira taron don su fahimci a ina ne gizo yake sakar don warwarewa.
“Mun kira ku ne a yau domin abin da ya zama baro-baro a fili ga kowa, abin da yake gaban kowa a yanzu, abin da ya addabi kowane dan Nijeriya a yau.
Kafin majalisa mu tafi hutu a makon da ya gabata mun tattauna a kan yanayin tsaro a kasar nan, kuma kafin nan ma mun sha yi.
“Tun da aka dawo mulkin dimokuradiyya a kasar daga 1999 babu wata gwamnati da ta zuba makudan kudi a harkar tsaro kamar gwamnati mai ci… duk da mun san babu wata kasa da za ta ce tana da tsaro dari bisa dari amma akwai yanayin da in aka shiga babu wata kasar da hankalinta zai kwanta. A gaskiya yanayin namu ya tsawaita.
Mun sa ran cewa zuwa yanzu an samu saukin lamarin, kuma Nijeriya ta samu ci gaba ba kawai a sha’anin tsaron ba har da tattalin arziki.
Na yi ammanar rundunonin tsaro suna bakin kokarinsu amma a zahirin gaskiya ya kamata mu kara himma.” In ji shi.
Majalisar ta bayyana cewa daga yau (Laraba) tana so ta fara ganin sauyi a sha’anin tsaron kasar.
Da yake nasa jawabin, Janar Irabo ya gode wa majalisar bisa gayyatar su da ta yi domin tattauna matsalar, inda ya ce, “Na yi amannar cewa bisa hikimar da shugaban majalisa da sauran masu taimaka masa suke da ita ta tara wannan taro saboda yanayin tsaron kasa za a samu mafita. Domin duk yanayi ko halin da aka shiga akwai sararin da za a iya musanyar ra’ayoyi da fasahohi domin kowa ya bayar da gudunmawarsa a kai”.
Ya ce akwai abubuwa da dama da suka aiwatar kuma akwai karin wasu
da suka sa a gaba wanda ake sa ran su taimaka wajen samun nasara.
Daga bisani dai sun ci gaba da ganawarsu cikin sirri inda aka kulle wa ‘yan jarida kofa.