Shalƙwatar tsaron Nijeriya (DHQ) ta bayyana wasu ‘yan ta’adda tara da ake nema, ciki har da Abu Khadijah, Abdurrahman, Dadi Gumba (wanda aka fi sani da Abu Muhammed), Usman Kanin Shehu, Abu Yusuf, Musa Wa’a, Ibrahim Suyeka, BA Sulhu, da Idris Taklakse.
Duk da babu wani lada da aka sanya kan su ga wanda ya tona asirinsu, DHQ na wannan yunƙuri ne sakamakon ƙaruwar barazanar tsaro a Arewacin Nijeriya.
- Jami’ai 3 Da Sojoji 22 ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Neja -DHQ
- Muna Gargadin Masu Cewa Mu Yi Juyin Mulki A Nijeriya – DHQ
Manjo Janar Edward Buba, Daraktan yaɗa labarai ne ya bayyana ɓulluwar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna ‘Lukarawas.’ An ruwaito cewa wannan ƙungiyar ta shiga jihohin Sokoto da Kebbi daga Jamhuriyar Nijar, bayan juyin mulkin da ya kawo tsaiko a haɗin kan Sojojin Nijeriya da Nijar kafin daga bisani a daidaita. ‘Yan ta’addan sun yi amfani da rashin haɗin gwuiwa don shigowa ta Arewa maso yammacin Nijeriya ta yankuna masu wahalar bi.
Buba ya bayyana cewa al’ummar yankin sun fara karɓar ƙungiyar ba tare da zargi ko kai rahoton ayyukansu ba. Ya tabbatar da cewa an fara ayyukan Soja na leƙen asiri don magance barazanar, yana mai cewa Sojoji na kan faɗaɗa ayyukansu don tabbatar da tsaro a yankunan da abin ya shafa.