A Jihar Kwara wata sabuwar ƙungiyar ‘yan bindiga mai suna ‘Mahmuda’ ta fara zama barazana ga zaman lafiya a yankin.
Wannan ƙungiya, wacce ke iƙirarin jihadi, na kai hare-hare a ƙananan hukumomin Kaiama da Baruten, tare da haddasa tsoro da gudun hijira ga mazauna yankunan.
- Gwamnan Edo Ya Dakatar da Sarki Saboda Matsalar Tsaro A Yankinsa
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababbun Shugabannin Gabon Da Ecuador
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ƙungiyar sun samu mafaka a gandun dajin Kainji Lake National Park, kuma daga nan ne suke fita su kai hare-hare a ƙauyukan Jihar Kwara har zuwa wasu sassan Jihar Neja.
Saboda haka, mutane da dama sun bar gidajensu suna tserewa zuwa wasu wuraren domin gujewa hatsari.
A cewar wasu mazauna yankin, ƙungiyar Mahmuda ta fara bayyana kimanin shekaru uku da suka gabata, inda suka kafa sansani a yankin, amma a wancan lokacin ba su hana mutane gudanar da rayuwarsu ba.
Sai dai daga baya suka fara yawo da makamai suna kama mutane, suna yanke musu hukunci har da kashe wasu.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa a yanzu mutane ba sa iya zuwa gonakinsu da ke nisan da kilomita biyu saboda tsoron ‘yan ƙungiyar.
Ya ce kashi 50 cikin 100 na mutanen garin sun tsere.
Baya ga haka, ƙungiyar ta haramta noma a yankin.
“Kashi 95 cikin 100 na mutanen manoma ne, amma yanzu sun ce ba za mu iya yin noma ba. Mutuwa tana kusa da mu saboda yunwa,” inji shi.
Wannan lamari na ƙara bayyana irin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a Nijeriya, musamman a jihohin da ake kyautata zaton sun fi samun kwanciyar hankali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp