Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Laraba, 19 ga watan Yuli, 2023 a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye a madadin gwamna Abba Kabir Yusif.
Gwamnan wanda ya taya al’ummar musulmin duniya murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci, ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah ya karo zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunkasar tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da yin kyawawan dabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma hakuri da juna kamar yadda Annabinmu Muhammad SAW ya koyar.