A ranar 23 ga wata, Kirsty Coventry, wacce ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics ta kasa da kasa kwanan nan, ta yi hira ta musamman da wani shirin gidan talabijin na CCTV mai lakabin “High-End Interview” a birnin Lausanne na kasar Switzerland. Wannan ita ce hira ta farko da ta yi da kafar yada labarai tun bayan da ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics na duniya.
Coventry ta ce ya zama wajibi a kiyaye kima da kuzarin wasannin motsa jiki na Olympics, tare da kara kiyaye su da kuma karfafa su. Ta ce, tana fatan yin mu’amala mai zurfi da dukkan masu ruwa da tsaki a watanni masu zuwa, tare da haduwa tare wajen tsara fasalin aiki na nan gaba da kuma yin aiki tare don tabbatar da yiwuwarsa a zahiri.
A halin da ake ciki kuma, ta ce, tana matukar fatan sake ziyartar kasar Sin nan da wasu watanni masu zuwa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)