Tsohon dan wasan Liverpool Sadio Mane ya bar Bayern Munich ya koma Al-Nassr ta Saudiyya.
Dan wasan mai shekaru 31, ya zura kwallaye 12 a wasanni 38 da ya buga wa Munich a kakar wasa ta bana duk da cewa ya taka rawar gani a farko.
- Barcelona Ta Doke AC Milan A Wasan Sada Zumunta
- Nijar: Sojoji Sun Kame Manyan ‘Yan Siyasa Da Ministocin BazoumÂ
Haka kuma dan wasan na Senegal ya samu rashin fahimta da Leroy Sane bayan rashin nasara a wasansu na gasar zakarun Turai.
Rahotanni sun nuna cewa zakarun na Jamus sun yanke shawarar sallamar Mane tun bayan samun rashin fahimtar.
Shugaban Bayern Jan-Christian Dreesen ya ce tsohon dan wasan Southampton ya kulla yarjejeniya ta shekaru hudu da Al-Nassr.
“Bai samu damar bayar da gudunmawa kamar yadda mu dauka ba kuma shi da kansa ya yi fata ba,” in ji Dreesen.
“Wani lokaci al’amura ba sa tafiya kamar yadda kowa yake so, a ko yaushe ina da dangantaka mai kyau da shi kuma hakan zai ci gaba,” in ji kocin Bayern Munich Thomas Tuchel.
Al-Nassr ta sayi Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar a watan Disamba kuma sun dauko dan wasan tsakiya na Croatia Marcelo Brozovic, dan wasan Brazil Alex Telles da dan wasan tsakiyar Ivory Coast Seko Fofana a bana.